Zab 100
100
Waƙar Yabo
1Bari dukan duniya ta raira waƙar farin ciki ga Ubangiji!
2Ku yi wa Ubangiji sujada da murna,
Ku zo gabansa, kuna raira waƙoƙin farin ciki!
3Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Allah!
Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne,
Mu jama'arsa ne, mu garkensa ne.
4Ku shiga Haikalinsa da godiya,
Ku shiga wurinsa mai tsarki, ku yabe shi!
Ku gode masa, ku yabe shi!
5 #
1Tar 16.34; 2Tar 5.13; 7.3; Ezra 3.11; Zab 106.1; 107.1; 118.1; 136.1; Irm 33.11 Ubangiji nagari ne,
Ƙaunarsa madawwamiya ce,
Amincinsa kuwa har abada abadin ne.
Currently Selected:
Zab 100: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979