YouVersion Logo
Search Icon

Zab 93

93
Allah Sarki Ne
1Ubangiji sarki ne!
Yana saye da ɗaukaka, suturarsa ƙarfi ne.
Hakika duniya ta kahu sosai a inda take,
Ba kuwa za ta jijjigu ba.
2Kursiyinka, ya Ubangiji, ya kahu tun daga farko,
Kana nan tun fil azal.
3Ya Ubangiji, zurfafan teku suna ta da muryarsu,
Suna ta da muryarsu da ruri.
4Ubangiji yana mulki cikin Sama,
Mulkinsa mafifici ne,
Fiye da rurin teku,
Fiye da ikon raƙuman ruwan teku.
5Dokokinka dawwamammu ne, ya Ubangiji,
Haikalinka kuwa tsattsarka ne ƙwarai,
Har abada abadin.

Currently Selected:

Zab 93: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in