YouVersion Logo
Search Icon

Zab 91

91
Zama a Inuwar Mai Iko Dukka
1Duk wanda ya je wurin Maɗaukaki
Zai zauna lafiya,
Duk wanda yake zaune a inuwar Mai Iko Dukka,
2Ya iya ce wa Ubangiji,
“Kai ne kāriyata, da mai kiyaye ni!
Kai ne Allahna, a gare ka nake dogara!”
3Hakika zai kiyaye ka
Daga dukan hatsarorin da ka ɓoye,
Daga kuma dukan mugayen cuce-cuce.
4Zai rufe ka da fikafikansa,
Za ka zauna lafiya a ƙarƙashinsu.
Amincinsa zai tsare ka, ya kiyaye ka.
5Ba za ka ji tsoron hatsarori da dare ba,
Ko fāɗawar da za a yi maka da rana,
6Ko annobar da take aukowa da dare,
Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana.
7Mutum dubu za su fāɗi daura da kai,
Dubu goma kuma za su fāɗi dama da kai,
Amma kai, ba za a cuce ka ba.
8Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye.
9Domin ka ɗauka Ubangiji yake kiyaye ka,
Maɗaukaki ne yake tsaronka,
10To, ba bala'in da zai same ka,
Ba za a yi wa gidanka aikin ƙarfi da yaji ba.
11 # Mat 4.6; Luk 4.10 Allah zai sa mala'ikunsa su lura da kai,
Za su kiyaye ka duk inda za ka tafi.
12 # Mat 4.6; Luk 4.11 Za su ɗauke ka a hannuwansu,
Don kada ka buga ƙafarka a dutse.
13 # Luk 10.19 Za ka tattake zakoki da macizai,
Za ka tattake zakoki masu zafin rai
Da macizai masu dafi.
14Allah ya ce, “Zan ceci waɗanda suke ƙaunata,
Zan kiyaye waɗanda suka san ni.
15Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu,
Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala,
Zan cece su in girmama su.
16Zan ba su tsawon rai lada,
Hakika kuwa zan cece su.”

Currently Selected:

Zab 91: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in