1
Zab 91:2
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ya iya ce wa Ubangiji, “Kai ne kāriyata, da mai kiyaye ni! Kai ne Allahna, a gare ka nake dogara!”
Compare
Explore Zab 91:2
2
Zab 91:1
Duk wanda ya je wurin Maɗaukaki Zai zauna lafiya, Duk wanda yake zaune a inuwar Mai Iko Dukka
Explore Zab 91:1
3
Zab 91:15
Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu, Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala, Zan cece su in girmama su.
Explore Zab 91:15
4
Zab 91:11
Allah zai sa mala'ikunsa su lura da kai, Za su kiyaye ka duk inda za ka tafi.
Explore Zab 91:11
5
Zab 91:4
Zai rufe ka da fikafikansa, Za ka zauna lafiya a ƙarƙashinsu. Amincinsa zai tsare ka, ya kiyaye ka.
Explore Zab 91:4
6
Zab 91:9-10
Domin ka ɗauka Ubangiji yake kiyaye ka, Maɗaukaki ne yake tsaronka, To, ba bala'in da zai same ka, Ba za a yi wa gidanka aikin ƙarfi da yaji ba.
Explore Zab 91:9-10
7
Zab 91:3
Hakika zai kiyaye ka Daga dukan hatsarorin da ka ɓoye, Daga kuma dukan mugayen cuce-cuce.
Explore Zab 91:3
8
Zab 91:7
Mutum dubu za su fāɗi daura da kai, Dubu goma kuma za su fāɗi dama da kai, Amma kai, ba za a cuce ka ba.
Explore Zab 91:7
9
Zab 91:5-6
Ba za ka ji tsoron hatsarori da dare ba, Ko fāɗawar da za a yi maka da rana, Ko annobar da take aukowa da dare, Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana.
Explore Zab 91:5-6