YouVersion Logo
Search Icon

Zab 90

90
LITTAFI NA HUƊU
(Zab 90—106)
Allah Madawwami, Mutum mai Shuɗewa
1Ya Ubangiji, a koyaushe kai ne wurin zamanmu.
2Kafin a kafa tuddai,
Kafin kuma ka sa duniya ta kasance,
Kai Allah ne, Madawwami.
Ba ka da farko, ba ka da ƙarshe.
3Kakan sa mutane su koma yadda suke,
Su zama ƙura.
4 # 2Bit 3.8 A gare ka shekara dubu, kamar kwana ɗaya ne,
Kamar jiya ce wadda ta shige,
Gajeruwa ce kamar sa'a guda ta dare.
5Kakan kwashe mutane kamar yadda ambaliyar ruwa take yi,
Kamar mafarki suke, ba su daɗewa.
Kamar tsire-tsire suke waɗanda suke tsirowa da safe,
6Su yi girma har su yi huda,
Sa'an nan su yi yaushi su bushe da yamma.
7Mun halaka ta wurin fushinka,
Mun razana saboda hasalarka.
8Ka jera zunubanmu a gabanka,
Zunubanmu na ɓoye kuwa,
Ka sa su a inda za ka gan su.
9Fushinka ya gajerta tsawon ranmu,
Ranmu ya ƙare kamar ajiyar zuciya.
10Tsawon kwanakin ranmu duka a ƙalla shekara ce saba'in,
In kuwa muna da ƙarfi, shekara tamanin ne.
Duk da haka iyakar abin da waɗannan shekaru
Suke kawo mana, damuwa ce da wahala,
Nan da nan sukan wuce,
Tamu da ƙare.
11Wa ya san iyakar ikon fushinka?
Wa ya san irin tsoron da hasalarka za ta kawo?
12Ka koya mana mu sani ranmu na ɗan lokaci ne,
Domin mu zama masu hikima.
13Ya Ubangiji, sai yaushe za ka ji tausayinmu?
Ka ji tausayin bayinka!
14Ka cika mu da madawwamiyar ƙaunarka a kowace safiya,
Don mu raira waƙoƙin murna dukan kwanakin ranmu.
15Yanzu sai ka sa mu yi farin ciki mai yawa,
Kamar yadda ka sa muka yi baƙin ciki
A dukan shekarun nan, da muka sha wahala.
16Ka yarda mana, mu bayinka, mu ga ayyukanka masu girma,
Ka yardar wa zuriyarmu su ga ikonka mai girma.
17Ka yarda, albarkarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji Allahnmu.
Ka sa mu yi nasara game da dukan abin da za mu yi!
I, ka ba mu nasara a dukan abin da muke yi!

Currently Selected:

Zab 90: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in