Bible App logo
Search Icon

Zab 87

87
Fa'idar Zama a Urushalima
1Allah ya gina birninsa a bisa tsarkakan tuddai,
2Yana ƙaunar birnin Urushalima fiye da kowane wuri a Isra'ila.
3Ya birnin Allah, ka kasa kunne,
Ga abubuwan banmamaki da ya faɗa a kanka.
4“Sa'ad da na lasafta sauran al'umma da suke yi mini biyayya,
Zan sa Masar da Babila a cikinsu,
Zan ce da Filistiya, da Taya, da Habasha,
Su ma na Urushalima ne.”
5A kan Sihiyona kuwa za a ce,
“Dukan sauran al'umma nata ne.”
Maɗaukaki kuwa zai ƙarfafa ta.
6Ubangiji zai rubuta lissafin jama'o'i,
Ya sa su duka cikin jimilla ta Urushalima.
7Duk mazauna a wurin za su raira waƙa, su yi rawa,
Su ce, “Dukan maɓuɓɓugaina suna cikinka.”

Currently Selected:

Zab 87: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for Zab 87