Bible App logo
Search Icon

Zab 88

88
Kukan Neman Taimako
1Ya Ubangiji Allah, Mai Cetona,
Duk yini ina ta kuka,
Da dare kuma na zo gare ka.
2Ka ji addu'ata,
Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako!
3Wahala mai yawa ta auko mini,
Har ina gab da mutuwa.
4Ina daidai da sauran mutanen da suke gab da mutuwa,
Dukan ƙarfina ya ƙare.
5An yashe ni a cikin matattu,
Kamar waɗanda aka karkashe,
Suna kuma kwance cikin kaburburansu,
Waɗanda ka manta da su ɗungum,
Waɗanda taimakonka ya yi musu nisa.
6Ka jefar da ni cikin zurfin kabari,
Da cikin rami mafi zurfi, mafi duhu.
7Fushinka yana da nauyi a kaina,
An turmushe ni a cikin tuƙuƙinka.
8Ka sa abokaina su yashe ni,
Ka sa sun ware ni.
An kange ni, ba yadda zan kuɓuta.
9Idanuna sun raunana saboda wahala.
Ya Ubangiji, kowace rana ina kira gare ka,
Ina ta da hannuwana zuwa gare ka da addu'a!
10Kakan yi wa matattu mu'ujizai ne?
Sukan tashi su yabe ka?
11Akan yi maganar madawwamiyar ƙaunarka a kabari?
Ko amincinka a inda ake hallaka?
12Za a iya ganin mu'ujizanka a cikin duhu?
Ko kuwa alherinka a lahira?
13Ya Ubangiji, ina kira gare ka, neman taimako,
Kowace safiya nakan yi addu'a gare ka.
14Me ya sa ka yashe ni, ya Ubangiji?
Me ya sa ka ɓoye kanka daga gare ni?
15Tun ina ƙarami nake shan wahala,
Har ma na kusa mutuwa,
Na tafke saboda nauyin hukuncinka.
16Hasalarka ta bi ta kaina,
Tasar mini da kake ta yi, ta hallaka ni.
17Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa,
Ta kowace fuska, sun rufe ni.
18Ka sa har abokaina na kusa sun yashe ni,
Duhu ne kaɗai abokin zamana.

Currently Selected:

Zab 88: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for Zab 88