Bible App logo
Search Icon

Zab 83

83
Addu'a don A Hallaka Abokan Gāban Isra'ila
1Ya Allah, kada ka yi shiru,
Kada ka tsaya cik,
Ya Allah, kada kuma ka yi tsit!
2Duba, abokan gābanka suna tawaye,
Maƙiyanka sun tayar.
3Suna ta ƙulle-ƙulle a asirce gaba da jama'arka,
Suna shirya maƙarƙashiya gāba da waɗanda kake tsaronsu.
4Suna cewa, “Ku zo, mu hallakar da al'ummarsu,
Don a manta da Isra'ila har abada!”
5Suka yarda a kan abin da suka shirya,
Suka haɗa kai gāba da kai.
6Su ne mutanen Edom, da Isma'ilawa,
Da mutanen Mowab, da Hagarawa,
7Da mutanen Gebal, da na Ammon, da na Amalek,
Da na Filistiya, da na Taya.
8Assuriya ma ta haɗa kai da su,
Haɗa kai ke nan mai ƙarfi da zuriyar Lutu.
9 # L.Mah 7.1-23; L.Mah 4.6-22 Ka yi musu yadda ka yi wa Madayanawa,
Ka yi musu yadda ka yi wa Sisera
Da Yabin a Kogin Kishon,
10Waɗanda aka kora a Endor,
Gawawwakinsu kuwa suka ruɓe a ƙasa.
11 # L.Mah 7.25; L.Mah 8.12 Ka yi wa shugabannin yaƙinsu yadda ka yi wa Oreb da Ziyib,
Ka kori dukan masu mulkinsu yadda ka kori Zeba da Zalmunna,
12Waɗanda suka ce, “Za mu ƙwace ƙasar da take ta Allah, ta zama tamu.”
13Ya Allahna, ka warwatsa su kamar ƙura,
Ka warwatsa su kamar ciyayin da iska take hurawa.
14Kamar yadda wuta take cin jeji,
Kamar yadda harshen wuta yake ƙone tuddai,
15Ka runtume su da hadirinka,
Ka razanar da su da iskarka mai ƙarfi.
16Ya Ubangiji, ka sa kunya ta rufe su,
Don su so su bauta maka.
17Ka sa a kore su, a razanar da su har abada,
Ka sa su mutu, mutuwar ƙasƙanci!
18Ka sa su sani kai kaɗai ne Ubangiji,
Kai kaɗai ne mamallakin dukan duniya!

Currently Selected:

Zab 83: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for Zab 83