Zab 84
84
Sa Zuciya ga Haikali
1Ina ƙaunar Haikalinka ƙwarai,
Ya Allah Mai Iko Dukka!
2A can nake so in kasance!
Ina marmarin farfajiyar Haikalin Ubangiji.
Da farin ciki mai yawa zan raira waƙa ga Allah Mai Rai.
3Har ba'u ma sukan yi sheƙa,
Tsattsewa suna da sheƙunansu,
A kusa da bagadanka suke kiwon 'ya'yansu.
Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina, Allahna.
4Masu murna ne waɗanda suke zaune a Haikalinka,
Kullum suna raira yabonka!
5Masu murna ne waɗanda suka sami ƙarfinsu daga gare ka,
Su waɗanda suka ƙosa su kai ziyara a Dutsen Sihiyona.
6Sa'ad da suke ratsa busasshen kwari,
Sai ya zama maɓuɓɓugar ruwa,
Ruwan sama na farko yakan rufe wurin da tafkuna.
7Sukan yi ta ƙara jin ƙarfi a cikin tafiyarsu,
Za su kuwa ga Allahn alloli a Sihiyona!
8Ka ji addu'ata, ya Ubangiji Allah Mai Runduna,
Ka ji ni, ya Allah na Yakubu!
9Duba, ya Allah, kai ne garkuwarmu,
Ka dubi fuskar Sarkinmu, zaɓaɓɓenka.
10Kwana guda da za a yi a Haikalinka,
Ya fi kwana dubu da za a yi a wani wuri dabam.
Na gwammace in tsaya a ƙofar Haikalin Allahna,
Da in zauna a gidajen mugaye.
11Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja,
Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja,
Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.
12Masu farin ciki ne waɗanda suka dogara gare ka,
Ya Allah Mai Runduna!
Currently Selected:
Zab 84: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979