Bible App logo
Search Icon

Zab 82

82
Tsautawa a kan Muguwar Shari'a
1Allah yana matsayinsa a taron jama'arsa,
Yakan zartar da nufinsa a taron alloli.
2Tilas ku daina yin rashin gaskiya a shari'a,
Ku daina goyon bayan mugaye!
3Ku kāre hakkin talakawa da na marayu,
Ku yi adalci ga matalauta,
Da waɗanda ba su da mataimaki.
4Ku kuɓutar da talakawa da matalauta,
Ku cece su daga ikon mugaye!
5“Waɗanne irin jahilai ne ku, wawaye!
Kuna zaune cikin duhu,
Ga shi, ba adalci a duniya sam!
6 # Yah 10.34 Na faɗa muku, ku alloli ne,
Cewa dukanku 'ya'ya ne na Maɗaukaki.
7Amma za ku mutu kamar kowane mutum,
Ku fāɗi kamar kowane basarauce.”
8Ya Allah, ka zo, ka mallaki duniya,
Dukan al'ummai naka ne.

Currently Selected:

Zab 82: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in