Bible App logo
Search Icon

Zab 79

79
Makoki saboda An Lalatar da Urushalima
1 # 2Sar 25.8-10; 2Tar 36.17-19; Irm 52.12-14 Ya Allah, arna sun fāɗa wa ƙasar jama'arka!
Sun ƙazantar da Haikalinka tsattsarka,
Sun bar Urushalima kufai.
2Suka bar wa tsuntsaye gawawwakin jama'arka su ci,
Suka bar wa namomin jeji gawawwakin bayinka.
3Suka zubar da jinin jama'arka kamar ruwa,
Jini ya yi ta gudu kamar ruwa
Ko'ina a Urushalima,
Ba ma wanda ya ragu don yă binne gawawwaki.
4Sauran al'ummar da take kewaye da mu,
Suka maishe mu abin ba'a, suka yi mana dariya,
Suka yi mana ba'a.
5Har yaushe za ka yi ta fushi da mu, ya Ubangiji?
Har abada ne?
Kullum ne fushinka zai yi ta ci kamar wuta?
6Ka yi fushi da al'umman da ba su yi maka sujada,
Ka yi fushi da jama'ar da suka ƙi ka!
7Sun karkashe mutanenmu,
Sun kuwa lalatar da ƙasarmu.
8Kada ka hukunta mu saboda zunuban kakanninmu,
Amma ka yi mana jinƙai yanzu,
Gama mun fid da zuciya sarai.
9Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu,
Saboda girmanka.
Ka cece mu, ka gafarta mana zunubanmu,
Don mutane su yabe ka.
10Don me al'ummai za su tambaye mu cewa,
“Ina Allahnku?”
Bari mu ga ka hukunta al'ummai
Saboda sun zubar da jinin bayinka!
11Ka kasa kunne ga nishin 'yan sarƙa,
Ka kuɓutar da waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa,
Ta wurin ikonka mai girma.
12Ya Ubangiji, ka rama wa al'umman nan har sau bakwai,
Saboda tsiwace-tsiwacen da suka yi maka.
13Mu waɗanda muke jama'arka, tumakin garkenka,
Za mu gode maka, mu yabe ka har abada.

Currently Selected:

Zab 79: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for Zab 79