Bible App logo
Search Icon

Zab 80

80
Addu'ar Komo da Al'umma
1 # Fit 25.22 Ka kasa kunne gare mu, ya Makiyayin Isra'ila,
Ka ji mu, kai da kake shugaban garkenka,
Da kake zaune a kan kursiyinka, a bisa kerubobi.
2Ka bayyana ƙaunarka ga kabilar Ifraimu,
Da ta Biliyaminu, da ta Manassa!
Ka nuna mana ikonka,
Ka zo ka cece mu!
3Ka komo da mu, ya Allah!
Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!
4Har yaushe ke nan ya Ubangiji Allah Mai Runduna,
Za ka yi ta fushi da addu'o'in jama'arka?
5Ka ciyar da mu da hawaye,
Ka shayar da mu da babban ƙoƙo na hawaye.
6Ka bar al'umman da take makwabtaka da mu
Su yi ta faɗa a kan ƙasarmu,
Abokan gābanmu kuma suna yi mana ba'a.
7Ka komo da mu, ya Allah Mai Runduna!
Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!
8Ka fito da kurangar inabi daga cikin Masar,
Ka kori sauran al'umma,
Ka dasa kurangar a ƙasarsu.
9Ka gyara mata wuri don ta yi girma,
Saiwoyinta suka shiga ƙasa sosai,
Ta yaɗu, ta rufe dukan ƙasar.
10Ta rufe tuddai da inuwarta,
Ta rufe manya manyan itatuwan al'ul da rassanta.
11Rassanta sun miƙe har Bahar Rum,
Har zuwa Kogin Yufiretis.
12Me ya sa ka rushe shingen da yake kewaye da ita?
Ga shi yanzu, duk mai wucewa yana iya satar 'ya'yanta.
13Aladen jeji kuma za su tattake ta,
Namomin jeji duka za su cinye ta.
14Ka juyo wurinmu, ya Allah Mai Runduna!
Daga Sama, ka dube mu,
Ka zo ka ceci kurangar inabinka!
15Ka zo ka ceci kurangar inabin nan
Wadda kai da kanka ka dasa,
Wannan ƙaramar kuranga,
Ka sa ta yi girma, ta yi ƙarfi sosai!
16Abokan gābanmu sun sa mata wuta, sun sare ta,
Ka yi fushi da su, ka hallaka su!
17Ka kiyaye jama'arka wadda ka zaɓa,
Ka keɓe ta.
Al'umman nan wadda ka sa ta yi girma, ta yi ƙarfi sosai!
18Ba za mu ƙara rabuwa da kai ba,
Ka rayar da mu, mu kuwa za mu yabe ka.
19Ka komo da mu, ya Ubangiji Allah Mai Runduna!
Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!

Currently Selected:

Zab 80: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for Zab 80