Zab 7
7
Addu'ar Neman a Yi Adalci
1Ya Ubangiji, Allahna, na sami mafaka a wurinka,
Ka cece ni, ka tserar da ni daga dukan masu fafarata,
2Idan ba haka ba kuwa, za su ɗauke ni,
Su tafi da ni zuwa wurin da ba wanda zai cece ni,
A can za su yayyage ni kamar zaki.
3Ya Ubangiji, Allahna, idan na aikata ɗaya daga cikin waɗannan,
Wato idan na yi wa wani laifi,
4Idan na ci amanar abokina,
Ko kuwa in na gwada wa maƙiyi fin ƙarfi ba dalili,
5To, bari abokan gābana su fafare ni, su kama ni,
Bari su datse ni har ƙasa, su kuma kashe ni,
Su bar ni ƙasa, matacce!
6Ka tashi da fushinka, ya Ubangiji,
Ka kuma tashi ka yi gāba da hasalar abokan gābana!
Ka tashi, ka taimake ni, gama adalci kake so a yi.
7Ka tattaro dukan kabilun da suke kewaye da kai,
Ka yi mulki a kansu daga Sama.
8Ya Ubangiji, kai ne alƙalin dukan mutane.
Ka shara'anta mini bisa ga adalcina,
Gama ba ni da laifi, ina kuma da kirki.
9 #
W.Yah 2.23
Ka tsai da muguntar mugaye,
Ina roƙonka, ka sāka wa mutanen kirki.
Kai Allah mai adalci ne,
Kana kuwa auna tunanin mutane, da marmarinsu.
10Allah ne mai kiyaye ni,
Yakan ceci waɗanda suke yi masa biyayya.
11Allah alƙali ne mai adalci,
Kullum kuwa yana kā da mugaye.
12Idan mutane ba su tuba ba,
Allah zai wasa takobinsa,
13Zai ɗana bakansa ya shirya shi,
Zai ɗauki makamansa masu dafi,
Ya kuma auna kibansa masu wuta.
14Ka duba, yadda mugu yake tunanin mugunta a ransa,
Yana shisshirya wahala, yana kuma aikata ruɗi.
15Yana haƙa rami mai zurfi a ƙasa,
Sa'an nan yă fāɗa ramin da ya haƙa!
16Saboda haka muguntarsa ta hukunta shi ke nan,
Rikicin kansa ya yi masa lahani.
17Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa,
Zan raira yabbai ga Ubangiji, Maɗaukaki.
Currently Selected:
Zab 7: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979