Bible App logo
Search Icon

Zab 8

8
Ɗaukakar Allah da Martabar Mutum
1Ya Ubangiji, Ubangijinmu,
An san girmanka ko'ina a dukan duniya.
Yabonka ya kai har sammai,
2 # Mat 21.16 Yara da jarirai suna raira shi,
Ka gina kagara saboda magabtanka,
Domin ka tsai da maƙiyanka da abokan gābanka.
3Sa'ad da na duba sararin sama, wanda ka yi,
Da wata da taurari waɗanda ka sa a wuraren zamansu,
4 # Ayu 7.17,18; Zab 144.3; Ibr 2.6-8 Wane ne mutum, har da kake tunawa da shi,
Mutum kurum, har da kake lura da shi?
5Duk da haka in banda kai ba wanda ya fi shi,
Ka naɗa shi da daraja da girma!
6 # 1Kor 15.27; Afi 1.22; Ibr 2.8 Ka sa shi ya yi mulkin dukan abin da ka halitta,
Ka ɗora shi a kan dukan abubuwa,
7Tumaki da shanu, har ma da namomin jeji,
8Da tsuntsaye da kifaye,
Da dukan halittar da suke cikin tekuna.
9Ya Ubangiji, Ubangijinmu,
An san girmanka ko'ina a dukan duniya!

Currently Selected:

Zab 8: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in