1
Zab 66:18
Littafi Mai Tsarki
HAU
Da ban watsar da zunubaina ba, Da Ubangiji bai ji ni ba.
Compare
Explore Zab 66:18
2
Zab 66:20
Ina yabon Allah, Domin bai ƙi addu'ata ba, Bai kuwa hana mini madawwamiyar ƙaunarsa ba.
Explore Zab 66:20
3
Zab 66:3
Ku faɗa wa Allah cewa, “Al'amuran da kake aikatawa Suna da banmamaki ƙwarai! Ikonka yana da girma ƙwarai, Har maƙiyanka sukan durƙusa a gabanka don tsoro.
Explore Zab 66:3
4
Zab 66:1-2
Ku yabi Allah da babbar murya ta farin ciki, Ya jama'a duka! Ku raira waƙar darajar sunansa, Ku yabe shi da ɗaukaka!
Explore Zab 66:1-2
5
Zab 66:10
Ka jarraba mu, ya Allah, Kamar yadda ake tace azurfa da wuta, Haka nan ka jarraba mu.
Explore Zab 66:10
6
Zab 66:16
Ku zo ku ji, dukanku, ku da kuke girmama Allah, Ni kuwa zan faɗa muku abin da ya yi mini.
Explore Zab 66:16