Zab 37
37
Makomar Mugaye da ta Nagargaru
1Kada ka damu saboda mugaye,
Kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba.
2Za su shuɗe kamar busasshiyar ciyawa,
Za su mutu kamar yadda tsire-tsire suke bushewa.
3Ka dogara ga Ubangiji ka aikata nagarta,
Ka zauna a ƙasar, ka sami lafiya.
4Ka nemi farin cikinka a wurin Ubangiji,
Zai kuwa biya maka bukatarka.
5Ka miƙa kanka ga Ubangiji,
Ka dogara gare shi, zai kuwa taimake ka.
6Zai sa nagartarka ta haskaka kamar haske,
Adalcinka kuma yă haskaka kamar tsakar rana.
7Ka natsu a gaban Ubangiji,
Ka yi haƙuri, ka jira shi,
Kada ka damu da waɗanda suke da dukiya,
Ko su da suka yi nasara da aikata mugayen shirye-shiryensu.
8Kada ka yi fushi, kada ka hasala!
Kada ka damu! Gama ba zai yi maka amfanin kome ba.
9Waɗanda suka dogara ga Ubangiji,
Za su yi zamansu lafiya a ƙasar,
Amma za a kori mugaye.
10A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe,
Za ka neme su, amma ba za a same su ba,
11 #
Mat 5.5
Amma masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar,
Su ji daɗin cikakkiyar salama.
12Mugu yakan yi wa mutumin kirki makarƙashiya,
Yana harararsa da ƙiyayya.
13Ubangiji yana yi wa mugu dariya,
Domin Ubangiji ya sani ba da daɗewa ba mugun zai hallaka.
14Mugaye sun zare takuba,
Sun tanƙware bakkunansu
Don su kashe matalauta da masu bukata,
Su karkashe mutanen kirki.
15Amma takubansu za su sassoke su,
Za a kakkarya bakkunansu.
16Ƙanƙanen abin da mutumin kirki yake da shi,
Ya fi dukan dukiyar mugaye amfani,
17Gama Ubangiji zai raba mugaye da ƙarfinsu,
Amma zai kiyaye mutanen kirki.
18Ubangiji yana kula da masu yi masa biyayya,
Ƙasar kuwa za ta zama tasu har abada.
19Ba za su sha wahala a lokacin tsanani ba,
Za su sami yalwa a lokacin yunwa.
20Amma mugaye za su mutu,
Magabtan Ubangiji kuwa za su shuɗe kamar furen jeji,
Za su ɓace kamar hayaƙi.
21Mugu yakan ci bashi, yă ƙi biya,
Amma mutumin kirki mai alheri ne,
Mai bayarwa hannu sake.
22Waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka,
Za su zauna lafiya lau a ƙasar,
Amma waɗanda ya la'anta
Za a kore su su fita.
23Ubangiji yakan bi da mutum lafiya
A hanyar da ya kamata yă bi,
Yakan ji daɗin halinsa,
24In ya fāɗi, ba zai yi warwar ba,
Gama Ubangiji zai taimake shi
Yă tashi tsaye.
25Yanzu dai na tsufa, ni ba yaro ba ne,
Amma ban taɓa ganin Ubangiji ya yar da mutumin kirki ba,
Ko kuma a ga 'ya'yansa suna barar abinci.
26A koyaushe yakan bayar a sake,
Yana ba da rance ga waɗansu,
'Ya'yansa kuwa dalilin albarka ne.
27Ka rabu da mugunta ka aikata nagarta,
Za ka kuwa zauna a ƙasar har abada,
28Gama Ubangiji yana ƙaunar abin da yake daidai,
Ba ya rabuwa da amintattun jama'arsa,
Yana kiyaye su koyaushe,
Amma za a kori zuriyar mugaye.
29Adalai za su yi zamansu lafiya a ƙasar,
Su gāje ta har abada.
30Kalmomin mutumin kirki suna da hikima,
Yana faɗar abin da yake daidai.
31Yakan riƙe dokar Allahnsa a zuciyarsa, Ba ya kauce mata, faufau.
32Mugu yakan yi fakon mutumin kirki,
Yă yi ƙoƙari yă kashe shi,
33Amma Ubangiji ba zai bar shi a hannun magabtansa ba,
Ko kuwa yă bari a kāshe shi
Sa'ad da ake masa shari'a.
34Ka sa zuciyarka ga Ubangiji
Ka kiyaye dokokinsa,
Shi zai ba ka ƙarfin da za ka mallaki ƙasar,
Za ka kuwa ga an kori mugaye.
35Na ga wani mugu, azzalumi,
Ya fi kowa tsayi,
Kamar itacen al'ul na Lebanon,
36Amma bayan ƙanƙanen lokaci,
Da na zaga, ban gan shi ba,
Na neme shi, amma ban same shi ba.
37Dubi mutumin kirki, ka lura da adali,
Mutumin salama yakan sami zuriya,
38Amma za a hallaka masu zunubi ƙaƙaf,
Za a kuma shafe zuriyarsu.
39Ubangiji yakan ceci adalai,
Ya kiyaye su a lokatan wahala.
40Yakan taimake su, yă kuɓutar da su,
Yakan cece su daga mugaye,
Gama sukan zo wurinsa don yă kāre su.
Currently Selected:
Zab 37: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979