1
Zab 37:4
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ka nemi farin cikinka a wurin Ubangiji, Zai kuwa biya maka bukatarka.
Compare
Explore Zab 37:4
2
Zab 37:5
Ka miƙa kanka ga Ubangiji, Ka dogara gare shi, zai kuwa taimake ka.
Explore Zab 37:5
3
Zab 37:7
Ka natsu a gaban Ubangiji, Ka yi haƙuri, ka jira shi, Kada ka damu da waɗanda suke da dukiya, Ko su da suka yi nasara da aikata mugayen shirye-shiryensu.
Explore Zab 37:7
4
Zab 37:3
Ka dogara ga Ubangiji ka aikata nagarta, Ka zauna a ƙasar, ka sami lafiya.
Explore Zab 37:3
5
Zab 37:23-24
Ubangiji yakan bi da mutum lafiya A hanyar da ya kamata yă bi, Yakan ji daɗin halinsa, In ya fāɗi, ba zai yi warwar ba, Gama Ubangiji zai taimake shi Yă tashi tsaye.
Explore Zab 37:23-24
6
Zab 37:6
Zai sa nagartarka ta haskaka kamar haske, Adalcinka kuma yă haskaka kamar tsakar rana.
Explore Zab 37:6
7
Zab 37:8
Kada ka yi fushi, kada ka hasala! Kada ka damu! Gama ba zai yi maka amfanin kome ba.
Explore Zab 37:8
8
Zab 37:25
Yanzu dai na tsufa, ni ba yaro ba ne, Amma ban taɓa ganin Ubangiji ya yar da mutumin kirki ba, Ko kuma a ga 'ya'yansa suna barar abinci.
Explore Zab 37:25
9
Zab 37:1
Kada ka damu saboda mugaye, Kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba.
Explore Zab 37:1