Zab 38
38
Addu'ar Mai Shan Wuya
1Kada ka yi fushi har ka tsauta mini, ya Ubangiji!
Kada ka hukunta ni da fushinka!
2Ka hukunta ni, ka kuwa yi mini rauni,
Ka kuma buge ni har ƙasa.
3Saboda fushinka ina ciwo mai tsanani,
Duk jikina ya kamu da ciwo saboda zunubina.
4Ina nutsewa cikin ambaliyar zunubaina,
Ina jin nauyinsu, sun danne ni ƙasa.
5Saboda wawancina, miyakuna sun ruɓe, suna wari,
6An tanƙware ni, an ragargaza ni,
Ina ta kuka dukan yini.
7Ina fama da zazzaɓi,
Ina rashin lafiya ƙwarai.
8An ragargaza ni sarai, an kuwa ci nasara a kaina,
Na damu a zuciyata, ina nishi don zafi.
9Ka san bukatata, ya Ubangiji,
Kana jin dukan nishe-nishena.
10Zuciyata tana ɗar, ƙarfina ya ƙāre,
Idanuna sun dushe.
11Abokaina da maƙwabtana ba su ko zuwa kusa da ni, saboda miyakuna,
Har iyalina ma sun guje mini.
12Masu son kashe ni, sun haƙa mini tarkuna,
Masu so su cuce ni, suna barazanar lalatar da ni,
Yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.
13Kamar kurma nake, ba na iya ji,
Kamar kuma bebe, ba na iya magana.
14Ni kamar mutumin da ba ya iya amsawa nake, don ba na ji.
15Na dogara gare ka, ya Ubangiji,
Kai za ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna.
16Kada ka bar magabtana su yi murna saboda wahalata.
Kada ka bar su su yi kirari a kan faɗuwata!
17Ina gab da fāɗuwa,
Ina cikin azaba kullum.
18Na hurta zunubaina,
Sun cika ni da taraddadi.
19Magabtana lafiyayyu ne masu ƙarfi.
Waɗanda yake ƙina ba dalili, suna da yawa.
20Masu rama nagarta da mugunta,
Suna gāba da ni,
Domin ina ƙoƙarin aikata abin da yake daidai.
21Kada ka yashe ni, ya Ubangiji,
Kada ka rabu da ni, ya Allahna!
22Sai ka taimake ni yanzu, ya Ubangiji, Mai Cetona!
Currently Selected:
Zab 38: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979