Bible App logo
Search Icon

Zab 34

34
Yabo domin Kuɓuta
1Zan yi godiya ga Ubangiji kullayaumin,
Faufau ba zan taɓa fasa yabonsa ba.
2Zan yabe shi saboda abin da ya yi,
Da ma dukan waɗanda suke da tawali'u su kasa kunne, su yi murna!
3Ku yi shelar girman Ubangiji tare da ni,
Mu yabi sunansa tare!
4Na yi addu'a ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini,
Ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona.
5Waɗanda ake zalunta suka dube shi suka yi murna,
Ba za su ƙara ɓacin rai ba.
6Marasa galihu suka yi kira gare shi, ya kuwa amsa.
Ya cece su daga dukan wahalarsu.
7Mala'ikansa yana tsaron waɗanda suke tsoron Ubangiji,
Ya cece su daga hatsari.
8 # 1Bit 2.3 Ku gane da kanku yadda Ubangiji yake da alheri!
Mai farin ciki ne mutumin da ya sami kwanciyar rai a wurinsa!
9Ku yi tsoron Ubangiji ku jama'arsa duka,
Masu tsoronsa suna da dukan abin da suke bukata.
10Har zakoki sukan rasa abinci su ji yunwa,
Amma masu biyayya ga Ubangiji,
Ba abu mai kyau da sukan rasa.
11Ku zo, ku abokaina, ku kasa kunne gare ni,
Zan koya muku ku ji tsoron Ubangiji.
12 # 1Bit 3.10-12 Kuna so ku ji daɗin rai?
Kuna son tsawon rai da farin ciki?
13To, ku yi nisa da mugun baki,
Da faɗar ƙarairayi.
14Ku rabu da mugunta, ku aikata alheri,
Ku yi marmarin salama, ku yi ƙoƙarin samunta.
15Ubangiji yana lura da adalai,
Yana kasa kunne ga koke-kokensu,
16Amma yana ƙin masu aikata mugunta,
Saboda haka har mutanensu sukan manta da su.
17Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, yakan kuwa kasa kunne,
Yakan cece su daga dukan wahalarsu.
18Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai,
Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.
19Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa,
Amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka.
20 # Yah 19.36 Ubangiji yakan kiyaye shi sosai,
Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da zai karye ba.
21Mugunta za ta kashe mugu,
Waɗanda suke ƙin adalai za a hukunta su.
22Ubangiji zai fanshi bayinsa,
Waɗanda suka tafi wurinsa neman mafaka
Za a bar su da rai.

Currently Selected:

Zab 34: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in