1
Zab 34:18
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai, Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.
Compare
Explore Zab 34:18
2
Zab 34:4
Na yi addu'a ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini, Ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona.
Explore Zab 34:4
3
Zab 34:19
Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa, Amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka.
Explore Zab 34:19
4
Zab 34:8
Ku gane da kanku yadda Ubangiji yake da alheri! Mai farin ciki ne mutumin da ya sami kwanciyar rai a wurinsa!
Explore Zab 34:8
5
Zab 34:5
Waɗanda ake zalunta suka dube shi suka yi murna, Ba za su ƙara ɓacin rai ba.
Explore Zab 34:5
6
Zab 34:17
Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, yakan kuwa kasa kunne, Yakan cece su daga dukan wahalarsu.
Explore Zab 34:17
7
Zab 34:7
Mala'ikansa yana tsaron waɗanda suke tsoron Ubangiji, Ya cece su daga hatsari.
Explore Zab 34:7
8
Zab 34:14
Ku rabu da mugunta, ku aikata alheri, Ku yi marmarin salama, ku yi ƙoƙarin samunta.
Explore Zab 34:14
9
Zab 34:13
To, ku yi nisa da mugun baki, Da faɗar ƙarairayi.
Explore Zab 34:13
10
Zab 34:15
Ubangiji yana lura da adalai, Yana kasa kunne ga koke-kokensu
Explore Zab 34:15
11
Zab 34:3
Ku yi shelar girman Ubangiji tare da ni, Mu yabi sunansa tare!
Explore Zab 34:3