Zab 35
35
Addu'ar Kuɓuta daga Maƙiya
1Ka yi hamayya da masu hamayya da ni, ya Ubangiji,
Ka yi faɗa da masu faɗa da ni!
2Ɗauki garkuwa da makamanka, ka zo ka taimake ni.
3Ka daga mashin yaƙinka sama, da gatarinka,
Ka yi gaba da masu fafarata.
Ka faɗa mini kai ne Mai Cetona!
4Ka sa a kori waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni, a kunyatar da su!
Ka sa waɗanda suke mini maƙarƙashiya su juya da baya, su ruɗe!
5Ka sa su zama kamar tattakar da iska take kwashewa,
Kamar waɗanda mala'ikan Ubangiji yake korarsu!
6Ka sa hanyarsu ta duhunta, ta yi santsi,
A sa'ad da mala'ikan Ubangiji yake fyaɗe su ƙasa!
7Suka kafa mini tarko ba dalili,
Sun kuma haƙa rami mai zurfi don in faɗa ciki.
8Amma kafin su farga, hallaka za ta kama su.
Tarkunan da suka kafa za su kama su,
Su kuma fāɗa cikin ramin da suka haƙa!
9Sa'an nan zan yi murna saboda Ubangiji,
Zan yi murna, gama ya cece ni.
10Da zuciya ɗaya zan ce wa Ubangiji,
“Ba wani kamarka!
Kakan kāre marasa ƙarfi daga masu ƙarfi,
Talaka da matalauci kuma daga azzalumai!”
11Mugaye suna ba da muguwar shaida a kaina,
Suna kai ƙarata a kan laifofin da ban san kome a kansa ba.
12Sun sāka mini alheri da mugunta,
Cike nake da nadama.
13Amma sa'ad da suke ciwo, nakan sa tufafin makoki,
Na ƙi cin abinci,
Na yi addu'a da kaina a sunkuye,
14Kamar yadda zan yi wa aboki ko ɗan'uwa addu'a.
Ina tafe a takure saboda makoki,
Kamar wanda yake makoki domin mahaifiyarsa.
15Sa'ad da nake shan wahala,
Murna suke yi duka,
Sun kewaye ni, suna ta yi mini dariya,
Baƙi sun duke ni, suna ta buguna.
16Suka wahalshe ni, suka yi mini dariya,
Suna hararata da ƙiyayya.
17Sai yaushe, za ka duba, ya Ubangiji?
Ka kuɓutar da ni daga farmakinsu,
Ka ceci raina daga waɗannan zakoki!
18Sa'an nan zan yi maka godiya a gaban babban taron jama'a.
Zan yabe ka a gaban babban taro.
19 #
Zab 69.4; Yah 15.25 Kada ka bar maƙiyana, maƙaryatan nan, su ga fāɗuwata!
Kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili,
Su ƙyaface ni, su yi murna saboda baƙin cikina!
20Ba su yin maganar zumunci,
A maimakon haka sukan ƙaga ƙarairayi a kan masu ƙaunar limana.
21Sukan zarge ni da kakkausan harshe,
Su ce, “Mun ga abin da ka yi!”
22Amma kai, ya Ubangiji ka ga wannan.
Saboda haka kada ka ƙyale su, ya Ubangiji,
Kada ka yi nisa!
23Ka tashi, ya Ubangiji, ka kāre ni.
Ya Allah ka tashi, ka bi mini hakkina.
24Kai mai adalci ne, ya Ubangiji, ka shaida rashin laifina,
Kada ka bar maƙiyana su ƙyaface ni, ya Allahna!
25Kada ka bar su su ce wa kansu,
“Madalla! Da ma abin da muke so ke nan!”
Kada ka bar su su ce,
“Mun rinjaye shi!”
26Ka sa waɗanda suka ƙyaface ni a wahalata,
A rinjaye su, su ruɗe.
Ka sa waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni,
Su sha kunya da wulakanci!
27Ka sa waɗanda suke murna da kuɓutata
Su yi ta sowa ta murna, suna cewa,
“Ubangiji mai girma ne!
Yana murna da cin nasarar bawansa!”
28Sa'an nan zan yi shelar adalcinka,
Dukan yini kuwa zan yi ta yabonka.
Currently Selected:
Zab 35: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979