Bible App logo
Search Icon

Zab 16

16
Gādon Alheri
1Ya Allah, ka kiyaye ni, gama na zo gare ka neman mafaka.
2Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Ubangijina,
Dukan kyawawan abubuwan da nake da su
Daga gare ka suke.”
3Dubi irin martabar da amintattun jama'ar Ubangiji suke da ita!
Ba abin da raina ya fi so,
Sai in zauna tare da su.
4Waɗanda suke hanzari zuwa ga gumaka,
Za su jawo wa kansu wahala.
Ba zan yi tarayya da su da hadayarsu ba.
Ba zan yi sujada ga gumakansu ba.
5Kai ne kaɗai, nake da shi, ya Ubangiji,
Kai ne kake biyan dukan bukatata,
Raina yana hannunka.
6Kyautanka zuwa gare ni da bansha'awa suke,
Kyawawa ne kuwa ƙwarai!
7Na yabi Ubangiji saboda yana bi da ni,
Da dare kuma lamirina yana yi mini fadaka.
8A kullum ina jin Ubangiji yana tare da ni,
Yana nan kusa, ba abin da zai girgiza ni.
9Don haka cike nake da murna da farin ciki,
Kullum kuwa ina jin kome lafiya yake,
10 # A.M 13.35 Saboda ba za ka yarda in shiga lahira ba,
Ba za ka bar wanda kake ƙauna a zurfafa daga ƙarƙas ba.
11 # A.M 2.25-28 Za ka nuna mini hanyar rai,
Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki,
Taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada.

Currently Selected:

Zab 16: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in