Zab 15
15
Mazauna a Tudun Allah Mai Tsarki
1Wane ne zai iya zama cikin Haikalinka?
Wa zai iya tsayawa a Sihiyona, wato tudunka tsattsarka?
2Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu,
Yana kuwa aikata abin da yake daidai,
Wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya,
3Wanda kuma ba ya ɓāta sunan waɗansu.
Ba ya zargin abokansa,
Ba ya kuwa baza jita-jita a kan maƙwabtansa.
4Yakan raina waɗanda Allah ya ƙi su,
Amma yana girmama waɗanda suke yi wa Ubangiji biyayya,
Kullum yana cika alkawaran da ya yi ko ta halin ƙaƙa,
5Yana ba da rance ba ruwa,
Ba ya karɓar hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi.
Wanda ya aikata waɗannan abubuwa ba zai taɓa fāɗuwa ba.
Currently Selected:
Zab 15: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979