YouVersion Logo
Search Icon

Zab 134

134
Kira a Yabi Allah
1Ku zo mu yabi Ubangiji,
Dukanku bayinsa,
Dukanku waɗanda kuke yi masa hidima,
A cikin Haikalinsa da dare.
2Ku ɗaga hannuwanku sama, ku yi addu'a a Haikali,
Ku yabi Ubangiji!
3Ubangiji wanda ya yi sama da duniya,
Ya sa muku albarka daga Sihiyona.

Currently Selected:

Zab 134: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in