YouVersion Logo
Search Icon

Zab 133

133
Yaba Ƙaunar 'Yan'uwanci
1Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma,
Ga jama'ar Allah su zauna tare kamar 'yan'uwa!
2Yana kama da man zaitun mai daraja,
Wanda yake naso daga bisa kan Haruna zuwa gemunsa,
Har zuwa wuyan riganunsa.
3Kamar raɓa a bisa Dutsen Harmon,
Wadda take zubowa a bisa tuddan Sihiyona.
A can ne Ubangiji ya alkawarta albarkarsa,
Rai na har abada.

Currently Selected:

Zab 133: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in