Zab 132
132
Yabo saboda Tsattsarkan Wuri
1Ya Ubangiji, kada ka manta da Dawuda
Da dukan irin aikin da ya yi.
2Ka tuna, ya Ubangiji, da alkawarin da ya yi,
Da rantsuwar da ya yi maka, ya Maɗaukaki, Allah na Isra'ila,
3“Ba zan tafi gida ko in kwanta ba,
4Ba zan huta, ko in yi barci ba,
5Sai sa'ad da na shirya wa Ubangiji wuri,
Wato Haikali domin Maɗaukaki, Allah na Isra'ila.”
6 #
2Tar 6.41,42 Mun ji labari akwatin alkawari yana Baitalami,
Amma muka same shi a kurmi.
7Muka ce, “Bari mu tafi Haikalin Ubangiji,
Mu yi sujada a gaban kursiyinsa!”
8Ka zo wurin hutawarka, ya Ubangiji,
Tare da akwatin alkawari,
Alama ce ta ikonka.
9Ka suturta firistoci da adalci,
Ka sa dukan jama'arka su yi sowa ta farin ciki!
10Ka yi wa bawanka Dawuda alkawari,
Kada ka rabu da zaɓaɓɓen sarkinka, ya Ubangiji!
11 #
2Sam 7.12-16; 1Tar 17.11-14; Zab 89.3,4; A.M 2.30 Ka yi wa Dawuda muhimmin alkawari,
Ba kuwa za ka ta da alkawarin ba.
Ka ce, “Za naɗa ɗaya daga cikin 'ya'yanka maza yă zama sarki,
Zai yi mulki a bayanka.
12Idan 'ya'yanka maza za su amince da alkawarina,
Da umarnan da na yi musu,
'Ya'yansu maza kuma za su bi bayanka su zama sarakuna,
A dukan lokaci.”
13Ubangiji ya yaɓi Sihiyona,
A can yake so ya gina Haikalinsa, ya ce,
14“A nan zan zauna har abada.
A nan kuma nake so in yi mulki.
15Zan tanada wa Sihiyona dukan abin da take bukata a yalwace,
Zan ƙosar da matalautanta da abinci.
16Zan sa firistocinta su yi shela,
Cewa ina yin ceto,
Jama'ata kuma za su raira waƙa,
Suna sowa don farin ciki.
17 #
1Sar 11.36
A nan ne zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Dawuda
Yake zama babban sarki,
A nan ne kuma zan wanzar da
Mulkin zaɓaɓɓen sarkina.
18Zan sa maƙiyansa su sha kunya,
Amma mulkinsa zai arzuta.
Ya kuma kahu.”
Currently Selected:
Zab 132: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979