Zab 131
131
Addu'ar Tawali'u
1'Ya Ubangiji, na rabu da girmankai,
Na bar yin fariya,
Ba ruwana da manyan al'amura,
Ba ruwana kuma da zantuttukan da suka fi ƙarfina.
2Amma na haƙura, raina a kwance,
Kamar jinjirin da yake kwance jalisan a hannun mahaifiyarsa,
Haka zuciyata take kwance.
3Ya Isra'ila, ka dogara ga Ubangiji,
Daga yanzu har abada!
Currently Selected:
Zab 131: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979