Zab 130
130
Sa Zuciya ga Ceton Allah
1A cikin fid da zuciyata,
Na yi kira gare ka, ya Ubangiji.
2Ka ji kukana, ya Ubangiji,
Ka kasa kunne ga kiran da nake yi na neman taimako!
3Idan kana yin lissafin zunubanmu,
Wa zai kuɓuta daga hukunci?
4Amma kakan gafarta mana,
Domin mu zama masu tsoronka.
5Na zaƙu, ina jiran taimako daga Ubangiji,
Ga maganarsa na dogara.
6Ina jiran Ubangiji,
Na zaƙu ƙwarai, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir,
I, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir.
7Ya Isra'ila, ki dogara ga Ubangiji,
Saboda ƙaunarsa madawwamiya ce,
A koyaushe yana da nufin yin gafara.
8 #
Mat 1.21; Tit 2.14 Zai fanshi jama'arsa Isra'ila
Daga dukan zunubansu.
Currently Selected:
Zab 130: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979