YouVersion Logo
Search Icon

Zab 129

129
Addu'a a kan Maƙiyan Isra'ila
1Isra'ila, sai ka faɗi irin muguntar
Da maƙiyanka suka tsananta maka da ita,
Tun kana ƙarami!
2“Maƙiyana suka tsananta mini da mugunta,
Tun ina ƙarami,
Amma ba su yi nasara da ni ba.
3Suka sa mini raunuka masu zurfi a bayana,
Suka mai da shi kamar gonar da aka nome.
4Amma Ubangiji mai adalci,
Ya 'yantar da ni daga bauta.”
5Allah ya sa duk waɗanda suke ƙin Sihiyona,
A yi nasara da su a kuma kore su!
6Allah ya sa su zama kamar ciyawar da take girma a kan soraye,
Ta kuwa bushe kafin ta isa yanka.
7Ba wanda zai tattara ta,
Ya ɗaure ta dami dami.
8Duk waɗanda suke wucewa a hanya ba za su ce,
“Ubangiji ya sa maka albarka!” ba,
Ko su ce, “Muna sa maka albarka da sunan Ubangiji!”

Currently Selected:

Zab 129: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in