Zab 128
128
Albarkar Mai Tsoron Ubangiji
1Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji,
Wanda yake zamansa bisa ga umarnansa!
2Za ka sami isasshen abin biyan bukatarka,
Za ka yi farin ciki ka arzuta.
3Matarka za ta zama kamar kurangar inabi
Mai 'ya'ya a gidanka,
'Ya'yanka maza kuma kamar dashen zaitun
Suna kewaye da teburinka.
4Mutumin da yake yi wa Ubangiji biyayya,
Hakika za a sa masa albarka kamar haka.
5Ubangiji ya sa maka albarka daga Sihiyona!
Ya sa ka ga Urushalima ta arzuta
Dukan kwanakinka!
6Ya kuma sa ka ka ga jikokinka!
Salama ta kasance ga Isra'ila!
Currently Selected:
Zab 128: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979