YouVersion Logo
Search Icon

Zab 127

127
Yabon Alherin Ubangiji
1Idan ba Ubangiji ne ya gina gidan ba,
Aikin magina banza ne.
Idan ba Ubangiji ne ya tsare birnin ba,
Ba wani amfani a sa matsara su yi tsaro.
2Ba wani amfani a sha wahalar aiki saboda abinci,
A yi asubancin tashi, a yi makarar kwanciya,
Gama Ubangiji yakan hutar da waɗanda yake ƙauna.
3'Ya'ya kyauta ne daga wurin Ubangiji,
Albarka ce ta musamman.
4'Ya'ya maza da mutum ya haifa a lokacin ƙuruciyarsa
Kamar kibau suke a hannun mayaƙi.
5Mai farin ciki ne mutumin da yake da irin waɗannan kibau da yawa!
Faufau ba za a ci nasara a kansa ba,
Sa'ad da ya kara da maƙiyansa a wurin shari'a.

Currently Selected:

Zab 127: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in