YouVersion Logo
Search Icon

Zab 124

124
Allah Ne Mai Ceton Jama'arsa
1Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu,
Da me zai faru?
Ba da amsa, ya Isra'ila!
2“Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu,
A lokacin da abokan gābanmu suka auka mana,
3Da sun haɗiye mu da rai a lokacin nan,
Saboda zafin fushi da suke yi da mu,
4Da rigyawa ta kwashe mu,
Da ruwa yi ci mu,
5Kwararowar ruwa ya nutsar da mu.”
6Sai mu gode wa Ubangiji,
Da bai bar abokan gābanmu su hallaka mu ba.
7Mun kuɓuta kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta,
Tarkon ya tsinke, mun 'yantu!
8Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa,
Shi wanda ya yi sama da duniya.

Currently Selected:

Zab 124: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in