Zab 125
125
Zaman Lafiyar Jama'ar Allah
1Waɗanda suke dogara ga Ubangiji,
Suna kama da Dutsen Sihiyona,
Wanda ba zai jijjigu ba, faufau.
Faufau kuma ba za a kawar da shi ba.
2Kamar yadda duwatsu suka kewaye Urushalima,
Haka nan Ubangiji zai kewaye jama'arsa,
Daga yanzu har abada.
3Ba a koyaushe mugaye za su yi mulki a ƙasar jama'ar Allah ba,
Idan kuwa suka yi, to, ya yiwu jama'ar Allah su yi laifi.
4Ya Ubangiji, ka yi wa mutanen kirki alheri,
Su waɗanda suke biyayya da umarnanka!
5Amma ka hukunta waɗanda suke bin mugayen al'amuransu,
Sa'ad da kake hukunta wa masu aikata mugunta!
Salama ta kasance tare da Isra'ila!
Currently Selected:
Zab 125: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979