Zab 111
111
Kiyayewar Ubangiji ga Jama'arsa
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Zan yi wa Ubangiji godiya da zuciya ɗaya,
A cikin taron jama'arsa.
2Abubuwan banmamaki ne Ubangiji yake aikatawa!
Duk waɗanda suke murna da su
Suna so su fahimce su.
3Dukan abin da yake yi,
Cike yake da girma da ɗaukaka,
Adalcinsa har abada ne.
4Ubangiji ba zai bar mu mu manta da ayyukansa masu banmamaki ba,
Shi mai alheri ne, mai jinƙai kuma.
5Yakan tanada wa masu tsoronsa abinci,
Bai taɓa mantawa da alkawarinsa ba.
6Ya nuna ikonsa ga jama'arsa
Saboda ya ba su ƙasashen baƙi.
7Iyakar abin da yake yi duka, da aminci da adalci ne.
Dukan umarnansa, abin dogara ne.
8Sukan tabbata har abada,
Da gaskiya da adalci aka ba da su.
9Ya kawo wa jama'arsa ceto,
Ya kuma yi musu madawwamin alkawari.
Mai Tsarki ne shi, Maɗaukaki!
10 #
Ayu 28.28; K.Mag 1.7; 9.10 Hanyar samun hikima, ita ce tsoron Ubangiji,
Yakan ba da kyakkyawar ganewa
Ga dukan waɗanda suke bin umarnansa,
Sai ku yabe shi har abada!
Currently Selected:
Zab 111: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979