Zab 110
110
Ubangiji Ya Ba Sarkin da Ya Zaɓa Iko
1 #
Mat 22.44; Mar 12.36; Luk 20.42,43; A.M 2.34,35; 1Kor 15.25; Afi 1.20-22; Kol 3.1; Ibr 1.13; 8.1; 10.12,13 Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina,
“Zauna nan a damana,
Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.”
2Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce,
“Ka yi mulki bisa maƙiyanka.”
3A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka,
Jama'arka za su kawo maka gudunmawa don kansu.
Kamar yadda raɓa take da sassafe,
Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka.
4 #
Ibr 5.6; 6.20; 7.17,21 Ubangiji ya yi muhimmin alkawari,
Ba kuwa zai fasa ba!
“Za ka zama firist har abada
Bisa ga tsabi'ar Malkisadik firist.”
5Ubangiji yana damanka,
Zai kori sarakuna a ranar da ya husata.
6Zai shara'anta wa dukan sauran al'umma,
Ya rufe fagen fama da gawawwaki,
Zai kori sarakunan duk duniya.
7Sarkin zai sha ruwan rafin da yake kan hanya,
Ya wartsake ya sami ƙarfi.
Zai yi tsayawar nasara.
Currently Selected:
Zab 110: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979