Zab 11
11
Mafakar Adalai
1Na dogara ga Ubangiji domin zaman lafiya,
Wauta ce idan kun ce mini,
“Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu,
2Domin mugaye sun ja bakkunansu,
Sun kuma ɗana kibansu
Domin su harbi mutanen kirki a duhu.
3Ba abin da mutumin kirki zai iya yi
Sa'ad da kome ya lalace.”
4Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa,
Yana da kursiyinsa a Sama.
Yana kallon dukan mutane
Yana sane da abin da suke yi.
5Yana auna masu kirki da mugaye dukka,
Yana ƙin marar bin doka gaba ɗaya.
6Yakan aukar da garwashin wuta
Da kibritu mai cin wuta a kan mugaye,
Yakan hukunta su da harshen wuta mai ƙuna.
7Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar kyawawan ayyuka,
Masu yi masa biyayya za su zauna a gabansa.
Currently Selected:
Zab 11: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979