Bible App logo
Search Icon

Zab 10

10
Addu'ar Neman Hamɓare Mugaye
1Ya Ubangiji, me ya sa kake can nesa?
Me ya sa ka ɓoye kanka a lokacin wahala?
2Mugaye suna fāriya, suna kuma tsananta wa matalauta,
Ɗana tarkon da suka yi yă kama su.
3Mugun mutum yana fāriya da mugayen manufofinsa,
Mai haɗama yakan zagi Ubangiji ya kuma ƙi shi.
4Mugun mutum da girmankansa yana cewa, “Ba Allah!”
Wannan ne abin da mugu yake tunani.
5Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.
Ba zai fahimci hukuncin Allah ba,
Yana yi wa abokan gābansa duban raini.
6Yana ce wa kansa “Ba zan taɓa fāɗuwa ba,
Ba zan taɓa shan wahala ba.”
7 # Rom 3.14 Maganganunsa suna cike da zage-zage, da ƙarairayi, da barazana,
Yana da saurin faɗar maganganun ƙiyayya da na mugunta.
8Yakan ɓuya cikin ƙauyuka,
Yă jira a can har yă kashe marasa laifi.
Yakan yi sanɗa, ya kama kāsassu,
9Yakan jira a inda ya ɓuya kamar zaki.
Yakan kwanta yana fakon wanda zai kama,
Har ya kama shi da tarkonsa ya tafi da shi!
10Yakan ragargaza kāsasshe,
Yă gwada masa ƙarfi, yă ci nasara a kansa.
11Mugun mutum yakan ce wa kansa, “Allah bai kula ba!
Ya rufe idonsa, ba zai taɓa ganina ba.”
12Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni!
Kada ka manta da waɗanda ake zaluntarsu, ya Allah!
13Yaya mugun zai riƙa raina Allah,
Har yă riƙa ce wa kansa, “Ba zai hukunta ni ba”?
14Amma kana gani, kana kuma lura da masu shan wuya, da masu ɓacin rai,
Koyaushe kuma a shirye kake ka yi taimako.
Mutum wanda ba shi da mai taimako yakan danka kansa gare ka,
Gama kullum kakan taimaki masu bukata.
15Ka karya ikon mugaye, masu mugunta,
Ka hukunta su saboda muguntarsu,
Har hukuncinsu ya cika sarai.
16Ubangiji sarki ne har abada abadin,
Arna kuma za su ɓace daga ƙasarsa.
17Za ka saurara ga addu'o'in masu kaɗaici, ya Ubangiji,
Za ka ba su ƙarfin hali.
18Za ka ji koke-koken waɗanda ake zalunta da na marayu,
Ka yi shari'ar da za su ji daɗi,
Domin kada 'yan adam su ƙara haddasa wata razana.

Currently Selected:

Zab 10: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in