Zab 101
101
Alkawarin Sarki domin Zaman Adalci
1Waƙata ta aminci ce da gaskiya.
Ina raira maka ita, ya Ubangiji.
2Abin da nake yi ba zai zama laifi ba,
Yaushe za ka zo wurina?
Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.
3Ba zan jure da mugunta ba ko kaɗan.
Na ƙi jinin ayyukan waɗanda suka bijire wa Allah,
Ba ruwana da su.
4Ba zan yi rashin aminci ba,
Ba kuwa zan yi tunanin mugunta ba.
5Zan hallakar da mai raɗar abokinsa,
Ba zan jure da mutum mai girmankai,
Ko mai alfarma ba.
6Zan yarda da waɗanda suke amincewa da Allah,
Zan yardar musu si yi zamansu a fādata,
Zan yarda wa waɗanda suke da tabbataccen aminci
Su yi mini hidima.
7Maƙaryaci ba zai zauna a fādata ba,
Ba zan yarda munafuki ya yi zamansa a wurina ba.
8A kowace rana zan yi ta karkashe dukan mugayen da suke cikin ƙasarmu,
Zan kori dukan mugaye daga birnin Ubangiji.
Currently Selected:
Zab 101: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979