1
Zab 1:1-2
Littafi Mai Tsarki
HAU
Albarka ta tabbata ga mutumin da Ba ya karɓar shawarar mugaye, Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi, Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah. Maimakon haka, yana jin daɗin karanta shari'ar Allah, Yana ta nazarinta dare da rana.
Compare
Explore Zab 1:1-2
2
Zab 1:3
Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama, Yakan ba da 'ya'ya a kan kari, Ganyayensa ba sa yin yaushi, Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.
Explore Zab 1:3
3
Zab 1:6
Gama Ubangiji yana lura da al'amuran adalai, Amma al'amuran mugaye za su watse.
Explore Zab 1:6