YouVersion Logo
Search Icon

K.Mag 23

23
1Sa'ad da ka zauna cin abinci tare da babban mutum, ka tuna da yadda yake. 2Idan kai mai son ci da yawa ne sai ka kanne. 3Kada ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da yake gabanku, zai yiwu wayo yake so ya yi maka.
4Ka zama mai isasshiyar hikima, kada ka gajiyar da kanka garin ƙoƙarin neman dukiya. 5Kuɗinka sun iya ƙarewa kamar ƙyiftawar ido, kamar suna da fikafikai su tashi kamar gaggafa.
6Kada ka ci abincin marowaci, ko ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da ya sa a gabanka. 7Zai ce, “Bari a ƙara maka,” amma ba haka yake nufi ba. Kamar gashi yake a cikin maƙogwaronka. 8Za ka harar da abin da ka ci, dukan daɗin bakinka zai tafi a banza.
9Kada ka yi wa wawa magana irin ta haziƙai, gama ba zai yaba da maganarka ba.
10Kada ka kuskura ka kawar da shaidar iyaka, ko ka ƙwace gonar marayu. 11Ubangiji Mai Iko shi ne kāriyarsu, shi zai yi magana dominsu.
12Ka mai da hankali ga malaminka, ka koyi dukan abin da kake iyawa.
13Kada ka bar yaro ba horo, gama ko ka duke shi ba za a kashe shi ba. 14Lalle ne za ka ceci ransa.
15Ɗana, idan ka zama mai hikima zan yi murna ƙwarai. 16Zan yi murna idan na ji kana faɗar magana da hikima.
17Kada ka yi ƙyashin masu aikata zunubi tsoron Ubangiji kaɗai za ka sa a gaba. 18Idan haka ta samu za ka yi farin ciki nan gaba.
19Ka saurara, ya ɗana, ka zama mai hikima. Ka yi tunani mai zurfi a kan hanyarka. 20Kada ka zauna da mashayan ruwan inabi, ko masu haɗama. 21Gama bugaggu da ruwan inabi da masu zarin ci za su zama matalauta. Idan iyakar abin da kake yi daga ci sai barci ne, nan da nan za ka ga kana saye da tsummoki.
22Ka kasa kunne ga mahaifinka, gama da ba dominsa ba, da ba ka, sa'ad da mahaifiyarka ta tsufa ka nuna mata godiyarka.
23Gaskiya, da hikima, da ilimi, da hankali, sun cancanta a saye su, kome tamaninsu.
24Mahaifin adali yana da dalilin yin murna. Zai yi fāriya a kan ɗa mai hikima.
25Ka sa mahaifinka da mahaifiyarka su yi fāriya da kai, ka sa mahaifiyarka farin ciki.
26Ɗana ka mai da hankali sosai, irin zamana ya zamar maka kyakkyawan misali. 27Karuwa, da mata mazinata, tarkon mutuwa ne su. 28Sukan laɓe su jira ka kamar mafasa, suna sa mutane da yawa su zama marasa aminci.
29Wa ake yi wa kaito? Wa yake da baƙin ciki? Wane ne mafaɗaci? Wa yake yin gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan ido? 30Sai riƙaƙƙen mashayi wanda yake gaurayar ruwan inabi. 31Kada ka bar ruwan inabi ya jarabce ka, ko da yake ja wur yake, har kana iya ganin kanka a cikin ƙoƙon, yana kuwa da kyan gani sa'ad da kake motsa shi. 32Kashegari za ka ji kamar maciji mai dafi ne ya sare ka. 33Idanunka za su riƙa gane-gane, ba za ka iya tunani ko ka faɗi magana sosai ba. 34Za ka ji kamar kana can cikin teku, jirin teku na ɗibarka kana lilo a kan rufin jirgin ruwa da yake tangaɗi. 35Za ka ce, “Lalle an doke ni, sosai an daddoke ni amma ban san lokacin ba, me ya sa ban farka ba? Ina bukatar in ƙara sha.”

Currently Selected:

K.Mag 23: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in