K.Mag 22
22
1Idan ya zama dole ne ka zaɓa tsakanin kyakkyawan suna ko dukiya, to, ka zaɓi kyakkyawan suna, tagomashi kuma ya fi azurfa da zinariya.
2Ba bambanci tsakanin mawadaci da matalauci, gama Ubangiji ne ya halicce su duka.
3Mutum mai hankali, in ya ga wahala tana zuwa yakan kauce mata, amma shashasha yakan kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.
4Kana da tsoron Ubangiji, ka yi tawali'u, za ka arzuta, ka ɗaukaka, ka sami tsawon rai.
5Idan kana ƙaunar ranka ka nisanci tarkunan da aka kafa a hanya don su kama mugaye.
6Ka koya wa yaro yadda zai yi zamansa, zai kuwa tuna da ita dukan kwanakinsa.
7Matalauta su ne bayin attajirai, bawa ne kai ga wanda ka ci bashi a gare shi.
8In ka shuka rashin gaskiya masifa ce za ta tsiro, wato hukunci mai tsanani wanda zai hallakar da kai.
9Ka zama mai hannu sake, ka riƙa ba matalauta abincinka, za a sa maka albarka saboda haka.
10Ka rabu da mutum mai fāriya, mai gardama, mafaɗaci, hatsaniya za ta ƙare.
11In ka yi ladabi za ka zama aminin sarki, gama yana ƙaunar amintaccen mutum.
12Ubangiji yana lura ya ga an riƙe gaskiya sosai ta wurin ƙin yarda da maganganun ƙarya.
13Malalaci yakan yi zamansa a gida, yakan ce, “Zaki zai kama ni in na fita waje.”
14Zina tarko ce, takan kama waɗannan waɗanda Ubangiji yake fushi da su.
15Halin yara ne su yi wauta da waɗansu abubuwa na rashin kula, amma tsumagiya za ta koya musu abin da ya fi kyau.
16Idan attajirai kake yi wa kyauta, kana kuma zaluntar matalauta don ka arzuta, kai kanka za ka talauce.
Umarnai da Dokoki
17Ka kasa kunne zan koya maka abin da masu hikima suka faɗa, yi nazari a kan koyarwarsu. 18Za ka yi murna in ka tuna da su, ka iya faɗarsu. 19Ina so ka dogara ga Ubangiji, don haka zan faɗa maka su yanzu. 20Na rubuta maka karin magana, suna ƙunshe da ilimi da kyakkyawar shawara. 21Zan koya maka ainihin gaskiya, domin sa'ad da aka aike ka ka nemo ta, za ka iya kawo amsa daidai.
22Kada ka ƙwari matalauci don ka fi shi, kada ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari'a. 23Ubangiji zai yi magana dominsu a kan shari'ar da suke yi, ya nemi ran duk wanda yake neman rayukansu.
24Kada ka yi abuta da mutane masu zafin fushi, ko masu zafin rai. 25Mai yiwuwa ne ka koyi irin ɗabi'unsu, har ka kasa sākewa.
26Kada ka yi alkawarin ɗaukar wa wani lamuni, 27gama idan ka kāsa biya har gadonka ma za su ɗauke.
28Kada ka kawar da shidar kan iyaka wadda kakanninka suka kafa.
29Ka nuna mini mutumin da yake aiki mai kyau, ni kuwa in nuna maka mutumin da ya fi duka, wanda ya cancanci ya zauna tare da sarakuna.
Currently Selected:
K.Mag 22: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979