YouVersion Logo
Search Icon

K.Mag 20

20
1Ruwan inabi da barasa sukan sa ka ka yi ta tā da murya, ka zama wawa. Wauta ce mutum ya bugu.
2Ka ji tsoron fushin sarki kamar yadda za ka ji tsoron zaki mai ruri, sa shi ya yi fushi kashe kai ne.
3Kowane wawa yakan fara yin jayayya, abin da ya fi daraja shi ne ka fita ka ware kanka.
4Manomin da ya cika lalaci, ya kasa nome gonakinsa a kan kari, a lokacin girbi ba zai sami kome ba.
5Tunanin mutum kamar ruwa yake a rijiya mai zurfi, sai mai basira ya iya ya jawo shi.
6Kowa gani yake shi mai biyayya ne, mai aminci. Amma ina? Ko ka yi ƙoƙari ka sami amintacce ɗaya daga cikinsu, ba za ka samu ba.
7'Ya'yan da mahaifinsu amintacce ne, wanda yake aikata abin da yake daidai, sun yi sa'a.
8Sarkin da yake yin shari'a ta gaskiya, da ganin mugunta ya san ta.
9Wane ne zai iya cewa lamirinsa garau yake, har da zai ce ya rabu da zunubinsa?
10Allah yana ƙin masu ma'aunin algus.
11Ayyukan da saurayi yake yi suke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta.
12Ubangiji ya ba mu ido don mu gani, ya ba mu kunne don mu ji.
13Idan barci ne sana'arka za ka talauce. Ka yi ta aiki za ka sami wadataccen abinci.
14Mai saye yakan yi kukan tsada a kullum, amma yakan tafi ya yi ta fāriya a kan ya iya ciniki.
15In ka san abin da kake faɗa, kana da wani abu wanda ya fi zinariya da lu'ulu'ai tamani.
16Sai wawa kaɗai yake ɗaukar lamunin biyan basusuwan da baƙo ya ci, ya kamata a karɓi dukiyarsa jingina.
17Abin da ka samu ta hanyar zamba kakan ji daɗinsa kamar abinci mai kyau, amma ko ba jima ko ba daɗe zai zama kamar yashi cike da bakinka.
18Ka nemi kyakkyawar shawara za ka yi nasara, kada ka jefa kanka cikin yaƙi ba tare da shiri ba.
19Mai baza jita-jita ba shi da asiri, ka yi nesa da mai yawan surutu.
20Idan ka zagi iyayenka, za ka mutu kamar fitilar da ta mutu cikin duhu.
21Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, amfaninta kaɗan ne.
22Kada ka ɗaukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji shi zai yi sakamako.
23Ubangiji yana ƙin waɗanda suke awo da ma'aunin algus.
24Ubangiji ya ƙayyade hanyoyinmu, ta ƙaƙa wani zai ce ya fahimci rai?
25Ka yi tunani a hankali kafin ka yi wa'adi za ka miƙa wa Allah wani abu, mai yiwuwa ne ka yi da na sani nan gaba.
26Sarki mai hikima zai bincika ya gane waɗanda suke aikata mugunta, ya hukunta su ba tausayi.
27Ubangiji ne ya ba mu hankali da lamiri, ba za mu iya ɓoye masa ba.
28Sarki zai zauna dafa'an cikin mulkinsa muddin yana mulki da aminci, da adalci, da daidaita.
29Ƙarfin samari abin darajantawa ne, furfurar tsofaffi abar girmamawa ce.
30Wani lokaci sai mun sha wuya muke sāke hanyoyinmu.

Currently Selected:

K.Mag 20: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in