K.Mag 19
19
1Gara mutum ya zama matalauci amma mai aminci, da a ce ya zama maƙaryaci, wawa.
2Yin ɗokin da ba ilimi ba shi da amfani, rashin haƙuri kuma zai jawo maka wahala.
3Waɗansu mutane sukan lalatar da kansu ta wurin ayyukansu na jahilci, sa'an nan su sa wa Ubangiji laifi.
4Attajirai sukan sami sababbin abokai a ko yaushe, amma matalauta ba zu su iya riƙon 'yan kaɗan da suke da su ba.
5Idan ka faɗi ƙarya a majalisa, za a hukunta ka, ba za ka kuɓuta ba.
6Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin manyan mutane, kowa na so a ce shi abokin mutumin nan ne, mai yawan alheri.
7'Yan'uwan matalauci ba su bukatarsa, ba abin mamaki ba ne ya rasa abokai. Kome ƙoƙarin da zai yi ba zai sami ko ɗaya ba.
8Ka yi wa kanka gatanci, ka koyi dukan abin da kake iyawa, sa'an nan ka tuna da abin da ka koya, za ka arzuta.
9Ba wanda zai faɗi ƙarya a majalisa ya rasa shan hukunci, maƙaryaci, tasa ta ƙare.
10Ko kusa wawaye ba za su yi zaman jin daɗi ba, haka nan kuma bayi ba za su yi mulki a kan iyayengijinsu ba.
11Mutum mai hankali yake danne fushinsa. Lokacin da wani ya cuce ka, abin kirki ne, ka yi kamar ba ka kula da shi ba.
12Hasalar sarki kamar rurin zaki ne, amma alherinsa kamar saukar ruwan sama ne.
13Dakikin ɗa yana jawo wa mahaifinsa lalacewa, mace mai mita tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.
14Mutum na iya cin gādon gida da kuɗi daga wurin iyayensa, amma Ubangiji ne kaɗai yake ba shi mace mai hankali.
15Rago, yi ta ragwancinka ka yi ta sharar barci, amma kai za ka sha yunwa.
16Ka kiyaye umarnai za ka rayu, in ka ƙi binsu kuwa za ka mutu.
17Sa'ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.
18Ka yi wa 'ya'yanka tarbiyya tun suna ƙanana yadda za su iya koyo. Idan ba ka yi haka ba, ka taimaka wajen lalacewarsu ke nan.
19Idan mutum mai zafin rai ne, ƙyale shi ya sha sakamakonsa. Idan ka fisshe shi daga cikin wahala sau ɗaya, sai ka sāke yi.
20Ka saurari shawara, ka yarda ka koya, wata rana za ka zama mai hikima.
21Mutum ya iya shirya dabaru iri iri, amma sai nufin Ubangiji ne zai tabbata.
22Abin kunya ne mutum ya zama mai haɗama, matalauci kuma ya fi maƙaryaci.
23Ka yi tsoron Ubangiji za ka yi tsawon rai, ka kuma sami biyan bukata, ba abin da zai cuce ka.
24Waɗansu mutane sun cika lalaci, ko abincinsu ba su iya taunawa.
25Za a hukunta mai fāriya saboda ya zama ishara ga mutanen da ba su san kome ba, mutum mai hikima yakan koya sa'ad da aka tsauta masa.
26Sai marar kunya, marar mutunci suke wulakanta mahaifinsa, ko ya kori mahaifiyarsa daga gidansa.
27Ɗana idan ka bar yin nazari za ka manta da abin da ka riga ka koya.
28Ba gaskiya ga mashaidin da ya yi niyyar cutar wani. Mugaye suna ƙaunar yin mugunta.
29Wawa mai fāriya hakika zai sha dūka.
Currently Selected:
K.Mag 19: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979