1
K.Mag 13:20
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima. Yi abuta da wawaye, za ka kuwa lalace.
Compare
Explore K.Mag 13:20
2
K.Mag 13:3
Ka lura da irin abin da kake faɗa don ka kiyaye ranka. Mutumin da bai kula da maganarsa ba, yakan hallakar da kansa.
Explore K.Mag 13:3
3
K.Mag 13:24
Idan ba ka horon ɗanka, ba ka ƙaunarsa ke nan, amma idan kana ƙaunarsa za ka riƙa kwaɓarsa.
Explore K.Mag 13:24
4
K.Mag 13:12
Idan ba bege, sai zuciya ta karai, amma muradin da ya tabbata zai cika ka da sa zuciya.
Explore K.Mag 13:12
5
K.Mag 13:6
Adalci yakan kiyaye marasa laifi, amma mugunta ita ce fāɗuwar masu zunubi.
Explore K.Mag 13:6
6
K.Mag 13:11
Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, za ka rasa ta da sauri, amma wanda ya same ta da wahala, za ta yi ta ƙaruwa.
Explore K.Mag 13:11
7
K.Mag 13:10
Fāriya ba ta kawo kome sai wahala. Hikima ce a nemi shawara.
Explore K.Mag 13:10
8
K.Mag 13:22
Mutumin kirki zai sami dukiya, har ya bar wa jikokinsa, amma dukiyar masu zunubi za ta zama ta adalai.
Explore K.Mag 13:22
9
K.Mag 13:1
Ɗa mai hikima yakan mai da hankali sa'ad da mahaifinsa yake kwaɓarsa, amma mutum mai girmankai ba ya yarda da kuskurensa.
Explore K.Mag 13:1
10
K.Mag 13:18
Mutumin da ba zai koya ba, zai talauce ya sha kunya, amma wanda ya kasa kunne ga tsautawa za a girmama shi.
Explore K.Mag 13:18
Home
Bible
Plans
Videos