K.Mag 11
11
1Ubangiji yana ƙin masu yin awo da ma'aunin zamba, amma yana farin ciki da masu yin awo da ma'auni na gaskiya.
2Masu girmankai za a kunyatar da su nan da nan. Hikima ce mutum ya zama mai kamewa.
3Mutanen kirki su ne gaskiya takan bi da su. Rashin aminci kuwa yana hallaka maciya amana.
4Dukiya ba ta da wani amfani a ranar mutuwa, amma adalci zai hana ka mutuwa.
5Gaskiya takan sa zaman mutanen kirki ya zama a sawwaƙe, amma mugun mutum shi yake kā da kansa da kansa.
6Adalci yakan ceci amintaccen mutum, amma marar aminci, haɗamarsa ce take zamar masa tarko.
7Mugun mutum yakan mutu da burinsa. Dogara ga dukiya bai amfana kome ba.
8Akan kiyaye adali daga wahala, amma takan auko wa mugu.
9Mutane sukan sha hasara ta wurin maganar marasa tsoron Allah, amma hikimar adalai takan yi ceto.
10Birni yakan yi farin ciki saboda wadatar mutanen kirki, akwai kuma sowa ta farin ciki sa'ad da mugaye suka mutu.
11Biranen da adalai suke cikinsu sukan ƙasaita, amma maganganun mugaye sukan hallakar da su.
12Wauta ce a yi wa waɗansu maganar raini, amma mutum mai la'akari yakan kame bakinsa.
13Ba wanda zai yarda ya faɗi asirinsa ga matsegunci, amma za ka amince wa amintaccen mutum.
14Al'ummar da ba ta da masu ja mata gora, za ta fāɗi. Yawan mashawarta yake kawo zaman lafiya.
15Wanda ya ɗaukar wa baƙo lamuni zai yi da na sani, zai fi maka sauƙi idan ba ruwanka.
16Mace mai mutunci abar girmamawa ce, amma azzalumai za su sami dukiya.
17In ka yi alheri, kanka ka samar wa tagomashi, in kuwa ka yi mugunta, kanka ka cutar.
18A ainihi mugaye ba su cin ribar kome, amma idan ka yi abin da yake daidai, ka tabbata za a sāka maka da alheri.
19Mutumin da ya yi niyyar aikata abin da yake daidai zai rayu, amma mutumin da ya dukufa ga aikata mugunta zai mutu.
20Ubangiji yana ƙin masu muguwar niyya, amma yana murna da waɗanda suke aikata abin da yake daidai!
21Ka tabbata fa za a hukunta mugaye, amma ba za a hukunta adalai ba.
22Kome kyan mace idan ba ta da kangado, tana kamar zoben zinariya a hancin alade.
23Abin da mutanen kirki suke so kullum yakan jawo alheri, idan mugaye sun sami biyan bukatarsu kowa zai yi ɓacin rai.
24Waɗansu mutane sukan kashe kuɗinsu hannu sake, duk da haka arzikinsu sai ƙaruwa yake yi. Waɗansu kuwa saboda yawan tsumulmularsu sukan talauce.
25Ka yi alheri za ka arzuta. Ka taimaki waɗansu, su kuma za su taimake ka.
26Mutane sukan la'anci mai ɓoye hatsi, yana jira ya yi tsada, amma sukan yabi wanda yake sayar da nasa.
27Idan nufe-nufenka na kirki ne za a girmama ka, amma idan kai mai neman tashin hankali ne, to, abin da zai same ka ke nan.
28Adalai za su arzuta, kamar ganyaye da bazara, amma waɗanda suke dogara ga dukiyarsu za su karkaɗe kamar ganyaye da kaka.
29Mutumin da yake jawo wa iyalinsa wahala, ƙarshensa talaucewa. Wawaye za su zama barorin masu hikima a ko yaushe.
30Adalci yana rayar da mutum, wanda yake da hikima kuma yakan ceci rayuka.
31 #
1Bit 4.18
Idan an sāka wa mutumin kirki da alheri a duniya, hakika za a hukunta wa mugaye da masu zunubi.
Currently Selected:
K.Mag 11: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979