K.Mag 10
10
Adali da Mugu Dabam Suke
1Karin maganar Sulemanu ke nan. Ɗa mai hikima abin fāriya ne ga mahaifinsa, amma wawa yakan jawo wa mahaifiyarsa baƙin ciki.
2Abin da ka samu ta hanyar zamba ba zai yi albarka ba, amma gaskiya za ta cece ka.
3Ubangiji ba zai bar mutumin kirki da yunwa ba, amma zai hana mugu ya kai ga biyan bukatarsa.
4Ragwanci zai sa talauci, amma yin aiki sosai zai arzuta ka.
5Mutum mai hankali yakan tattara amfanin gona da kaka, amma abin kunya ne a yi barci a lokacin girbi.
6Mutumin kirki yakan karɓi albarka, maganganun mugun kuwa sukan ɓoye mugun halinsa.
7Tunawa da mutumin kirki albarka ce, amma nan da nan za a manta da mugaye.
8Mutane masu hankali sukan bi shawarar kirki, masu maganar wauta kuwa za su lalace.
9Amintaccen mutum zai zauna lafiya ba abin da zai same shi, amma marasa aminci za a kama su.
10Mutumin da ya ƙi faɗar gaskiya yana haddasa wahala, amma wanda ya bayyana gaskiya zai kawo salama.
11Kalmomin mutumin kirki maɓuɓɓugan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.
12 #
Yak 5.20; 1Bit 4.8 Ƙiyayya takan haddasa wahala, amma ƙauna takan ƙyale dukan laifofi.
13Mutane masu fasaha sukan yi magana mai ma'ana, amma wawaye suna bukatar horo.
14Mutane masu hikima sukan nemi ilimi iyakar iyawarsu, amma sa'ad da wawa ya yi magana, wahala tana kusa.
15Wadata takan kiyaye attajiri, amma tsiya takan hallaka matalauci.
16Sakayyar da za a yi wa mutumin kirki ta rai ce, amma zunubi yakan sa a ƙara yin wani zunubi.
17Mutumin da yake kasa kunne sa'ad da ake kwaɓarsa zai rayu, amma duk wanda bai yarda da kuskurensa ba yana cikin hatsari.
18Mutumin da yake faɗar ƙarairayi maƙiyi ne, dukan wanda yake baza jitajita wawa ne.
19Bisa ga yawan surutunka, mai yiwuwa ne ƙwarai ka yi zunubi, amma idan kai mai la'akari ne, sai ka yi shiru.
20Kalmomin mutumin kirki suna kama da azurfa tsantsa, amma shawarwarin mugu ba su da wani amfani.
21Kalmomin mutumin kirki za su amfani mutane da yawa, amma kana iya hallaka kanka da wauta.
22Albarkar Ubangiji takan arzuta mutum, amma yawan aiki ba shi yake kawo arziki ba.
23Wawa ne yake jin daɗin aikata mugunta, amma mai fasaha yana jin daɗin hikima.
24Abin da mugun yake tsoro, shi yakan auko masa, amma adali yakan sami biyan bukatarsa.
25Hadiri yakan taso ya wargaza mugaye, amma amintattu lafiya lau suke a ko yaushe.
26Sam, kada ka sa malalaci ya yi maka wani abu, zai sa ka ka yi fushi, idanunka su cika da hawaye mai zafi.
27Ka yi tsoron Ubangiji za ka rayu, ka yi tsawon rai, amma mugaye sukan mutu tun kwanansu bai ƙare ba.
28Abin da mutanen kirki suke sa zuciya yakan kai su ga murna, amma mugaye ba su da wani abu da za su sa zuciya a kai.
29Ubangiji yana kiyaye marasa laifi, amma yakan hallaka masu mugunta.
30Kullayaumi adalai sukan yi zamansu lafiya, amma mugaye ba za su zauna a ƙasar ba.
31Maganar adalai ta hikima ce, amma harshen da yake hurta mugunta, za a dakatar da shi.
32Adalai sun san irin maganar da ta cancanta su faɗa, amma mugaye, kullum sukan faɗi maganar da za ta cutar.
Currently Selected:
K.Mag 10: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979