1
K.Mag 11:25
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ka yi alheri za ka arzuta. Ka taimaki waɗansu, su kuma za su taimake ka.
Compare
Explore K.Mag 11:25
2
K.Mag 11:24
Waɗansu mutane sukan kashe kuɗinsu hannu sake, duk da haka arzikinsu sai ƙaruwa yake yi. Waɗansu kuwa saboda yawan tsumulmularsu sukan talauce.
Explore K.Mag 11:24
3
K.Mag 11:2
Masu girmankai za a kunyatar da su nan da nan. Hikima ce mutum ya zama mai kamewa.
Explore K.Mag 11:2
4
K.Mag 11:14
Al'ummar da ba ta da masu ja mata gora, za ta fāɗi. Yawan mashawarta yake kawo zaman lafiya.
Explore K.Mag 11:14
5
K.Mag 11:30
Adalci yana rayar da mutum, wanda yake da hikima kuma yakan ceci rayuka.
Explore K.Mag 11:30
6
K.Mag 11:13
Ba wanda zai yarda ya faɗi asirinsa ga matsegunci, amma za ka amince wa amintaccen mutum.
Explore K.Mag 11:13
7
K.Mag 11:17
In ka yi alheri, kanka ka samar wa tagomashi, in kuwa ka yi mugunta, kanka ka cutar.
Explore K.Mag 11:17
8
K.Mag 11:28
Adalai za su arzuta, kamar ganyaye da bazara, amma waɗanda suke dogara ga dukiyarsu za su karkaɗe kamar ganyaye da kaka.
Explore K.Mag 11:28
9
K.Mag 11:4
Dukiya ba ta da wani amfani a ranar mutuwa, amma adalci zai hana ka mutuwa.
Explore K.Mag 11:4
10
K.Mag 11:3
Mutanen kirki su ne gaskiya takan bi da su. Rashin aminci kuwa yana hallaka maciya amana.
Explore K.Mag 11:3
11
K.Mag 11:22
Kome kyan mace idan ba ta da kangado, tana kamar zoben zinariya a hancin alade.
Explore K.Mag 11:22
12
K.Mag 11:1
Ubangiji yana ƙin masu yin awo da ma'aunin zamba, amma yana farin ciki da masu yin awo da ma'auni na gaskiya.
Explore K.Mag 11:1
Home
Bible
Plans
Videos