Neh 6
6
Sharrin 'Yan Hammayya
1Sa'ad da fa aka sanar da Sanballat, da Tobiya, da Geshem Balarabe, da sauran abokan gābanmu, cewa na gina garun, har ba sauran tsaguwa da ta ragu, ko da yake a lokacin ban riga na sa wa ƙofofi ƙyamare ba, 2sai Sanballat da Geshem suka aika wurina cewa, “Ka zo mu sadu a wani ƙauye a filin Ono,” amma da nufin su cuce ni.
3Sai na aika musu da manzanni, na ce, “Ina fama da babban aiki, ba ni da damar zuwa wurinku. Don me zan bar aiki in gangaro zuwa wurinku?”
4Suka yi ta aiko mini da wannan saƙo har sau huɗu, ni kuwa na yi ta ba su amsa irin ta dā.
5A karo na biyar sai Sanballat ya aiko da buɗaɗɗiyar wasiƙa ta hannun baransa, da irin maganar dā. 6Ga abin da yake cikin wasiƙar, “Geshem ya faɗa mini, ana ta ji jita jita wurin maƙwabta, cewa kai da Yahuduwa kuna niyyar tayarwar, don haka kake ginin garun, kana so kuma ka naɗa kanka sarki. 7Ga shi, ka sa annabawa su yi shelarka a Urushalima cewa, ‘Akwai sarki a Yahuza.’ To, za a faɗa wa sarki wannan magana, sai ka zo mu yi shawara tare a kan wannan al'amari.”
8Sai na mayar masa da amsa cewa, “Faufau, ba a yi wani abu haka kamar yadda ka faɗa ba, kai ne ka ƙaga wannan a zuciyarka.”
9Gama dukansu so suke su tsoratar da mu, suna cewa, “Za su daina aikin.” Amma na yi addu'a, na ce, “Ya Allah, ka ƙarfafa ni.”
10Sa'ad da na ziyarci Shemaiya ɗan Delaiya, wato jikan wanda aka hana shi fita, sai ya ce mini, “Bari mu tafi cikin Haikalin Allah, mu rufe ƙofofin Haikalin, gama suna zuwa su kashe ka, za su iya zuwa a wani dare su kashe ka.”
11Sai na ce, “Mutum kamata ne, zai gudu? Mutum irina zai shiga Haikali don ya tsere? To, ba zan tafi ba.”
12Na gane Allah bai aike shi wurina ba. Ya yi mini wannan magana domin Tobiya da Sanballat sun haɗa baki da shi. 13Gama da wannan nufi ne suka haɗa baki, don in ji tsoro, in yi yadda suke so, in yi zunubi, da haka za su ba ni mugun suna, su yi mini ba'a.
14“Ya Allahna, ka tuna da Tobiya da Sanballat bisa ga abubuwan nan da suka yi, da annabiya Nowadiya, da sauran annabawa waɗanda suka so su tsoratar da ni.”
Gamawar Aikin
15A cikin kwana hamsin da biyu aka gama garun, ran ashirin da biyar ga watan Elul. 16Sa'ad da abokan gābanmu da dukan al'umman da suke kewaye da mu suka ji, sai suka ji tsoro, gabansu kuma ya faɗi, gama sun gane, da taimakon Allahnmu muka yi wannan aiki.
17A kwanakin nan kuma shugabannin Yahuza suka yi ta aika wa Tobiya da wasiƙu, shi kuma Tobiya yana ta aika musu da nasa wasiƙu. 18Mutane da yawa a Yahuza sun rantse za su goyi bayan Tobiya, domin ya auri 'yar Shekaniya, ɗan Ara. Ɗansa kuma, wato Yohenan, ya auri 'yar Meshullam, ɗan Berikiya. 19Mutane suka yi magana a kan ayyukan kirki na Tobiya a gabana. Suka kuma kai maganata a wurinsa, sai Tobiya ya yi ta aika mini da wasiƙu don ya tsoratar da ni.
Currently Selected:
Neh 6: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979