YouVersion Logo
Search Icon

Neh 11

11
Mazaunan Urushalima
(1Tar 9.1-34)
1Shugabannin jama'a kuwa suka zauna a Urushalima. Sauran jama'a kuma suka jefa kuri'a don a sami mutum guda daga cikin goma wanda zai zauna a Urushalima, wato tsattsarkan birni, sauran tara kuwa su yi zamansu a sauran garuruwa. 2Jama'a suka sa wa dukan waɗanda suka tafi su zauna a Urushalima da yardar ransu albarka.
3 # Neh 7.73 Waɗannan su ne shugabannin lardi waɗanda suka zauna a Urushalima, amma a garuruwan Yahuza kowa ya zauna a mahallinsa a garuruwansu, wato Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da ma'aikatan Haikali, da zuriyar barorin Sulemanu.
4Waɗansu mutanen Yahuza da na Biliyaminu suka zauna a Urushalima.
Daga cikin mutanen Yahuza akwai Ataya ɗan Azariya, wato jīkan Zakariya ɗan Amariya. Sauran kakanninsa su ne Shefatiya, da Mahalalel, zuriyar Feresa ɗan Yahuza.
5Akwai kuma Ma'aseya ɗan Baruk, jīkan Kolhoze. Sauran kakanninsa su ne Hazaiya, da Adaya, da Yoyarib, da Zakariya, zuriyar Shela ɗan Yahuza.
6Dukan mutanen Feresa da suka zauna Urushalima su ɗari huɗu da sittin da takwas ne, dukansu kuwa muhimman mutane ne.
7Waɗannan su ne mutanen Biliyaminu, Sallai ɗan Meshullam, jīkan Yowed. Sauran kakanninsa su ne Fedaiya, da Kolaiya, da Ma'aseya, da Itiyel da Yeshaya.
8Sa'an nan kuma ga Gabbai da Sallai danginsa, mutum ɗari tara da ashirin da takwas. 9Yowel ɗan Zikri shi ne shugabansu, Yahuza ɗan Hassenuwa shi ne shugaba na biyu cikin birnin.
10Na wajen firistoci, su ne Yedaiya ɗan Yoyarib, da Yakin, 11da Seraiya ɗan Hilkiya, jīkan Shallum. Sauran kakanninsa, su ne Zadok, da Merayot, da Ahitub, mai lura da Haikalin Allah. 12Tar e da 'yan'uwansu waɗanda suka yi aiki a Haikali, su ɗari takwas da ashirin da biyu ne.
Akwai kuma Adaya ɗan Yeroham, jīkan Felaliya. Sauran kakanninsa su ne Amzi, da Zakariya, da Fashur, da Malkiya. 13Tare da 'yan'uwansu shugabannin gidajen kakanni, su ɗari da arba'in da biyu. Sai kuma Amashai ɗan Azarel, jīkan Azai. Sauran kakanninsa su ne Meshillemot, da Immer. 14Tare da 'yan'uwansu, su ɗari da ashirin da takwas ne gwarzayen sojoji ne. Shugabansu shi ne Zabdiyel ɗan Haggedolim.
15Na wajen Lawiyawa kuwa su ne Shemaiya ɗan Hasshub, jīkan Azrikam. Sauran kakanninsa su ne Hashabiya, da Bunni, 16da Shabbetai, da Yozabad, ɗaya daga cikin manyan shugabanni na Lawiyawa, waɗanda suke lura da kewayen Haikalin Allah. 17Da kuma Mattaniya ɗan Mika, jīkan Zikri, zuriyar Asaf, shi ne shugaba na farko na mawaƙan addu'a ta godiya. Bakbukiya, shi ne mataimakin Mattaniya. Ga kuma Obadiya ɗan Shemaiya, jīkan zuriyar Galal, zuriyar Yedutun. 18Dukan Lawiyawa da suke a tsattsarkan birni su ɗari biyu da tamanin da huɗu ne.
19Masu tsaron ƙofofi kuma su ne Akkub, da Talmon, da 'yan'uwansu, su ɗari da saba'in da biyu ne.
20Sauran jama'ar Isra'ila kuwa, da firistoci, da Lawiyawa suka zauna a dukan garuruwan Yahuza, kowa ya zauna a gādonsa. 21Amma ma'aikatan Haikali suka zauna a Ofel. Ziha da Gishfa, su ne shugabannin ma'aikatan Haikali.
22Shugaban Lawiyawan da yake a Urushalima, shi ne Uzzi ɗan Bani, jīkan Hashabiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, ɗan Mika daga zuriyar Asaf. Su ne mawaƙa a Haikalin Allah. 23Sarki ya yi wa shugabannin mawaƙa umarni da ƙarfi a kan abin da za su yi kowace rana.
24Fetahiya ɗan Meshezabel, daga zuriyar Zera na kabilar Yahuza, shi ne wakilin sarki a kan dukan abin da ya shafi jama'a.
Mutanen da Suke a Sauran Garuruwa da Birane
25Game da ƙauyuka da gonakinsu kuma, waɗansu mutanen Yahuza suka zauna a Kiriyat-arba, da Dibon da ƙauyukanta, da Yekabzeyel da ƙauyukanta, 26da a biranen Yeshuwa, da Molada, da Bet-felet, 27da Hazar-shuwal, da Biyer-sheba da ƙauyukanta, 28da Ziklag, da Mekona da ƙauyukanta, 29da En-rimmon, da Zora, da Yarmut, 30da Zanowa, da Adullam da ƙauyukansu, da Lakish da gonakinta, da Azeka da ƙauyukanta. Haka suka yi zango daga Biyer-sheba zuwa kwarin Hinnom.
31Mutanen kabilar Biliyaminu suka zauna a Geba, da Mikmash, da Ayya, da Betel da sauran ƙauyuka na kewaye, 32da Anatot, da Nob, da Ananiya, 33da Hazor, da Rama, da Gittayim, 34da Hadid, da Zeboyim, da Neballat, 35da Lod, da Ono, wato kwarin masu sana'a. 36Waɗansu kashi na Lawiyawan da suke a Yahuza, aka sa su zauna a yankin ƙasar Biliyaminu.

Currently Selected:

Neh 11: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy