YouVersion Logo
Search Icon

Neh 10

10
1Waɗanda suka fara sa hannu a takardar alkawarin, su ne mai mulki, wato Nehemiya ɗan Hakaliya, da Zadakiya, 2-8sa'an nan firistoci, wato
Seraiya, da Azariya, da Irmiya,
Fashur, da Amariya, da Malkiya,
Hattush, da Shebaniya, da Malluki,
Harim, da Meremot, da Obadiya,
Daniyel, da Ginneton, da Baruk,
Meshullam, da Abaija, da Miyamin,
Mawaziya, da Bilgai, da Shemaiya.
9-13Wajen Lawiyawa kuwa, su ne
Yeshuwa ɗan Azaniya, da Binnuyi daga zuriyar Henadad da Kadmiyel.
'Yan'uwansu kuwa su ne Shebaniya, da Hodiya,
Kelita, da Felaya, da Hanan,
Mika, da Rehob, da Hashabiya,
Zakkur, da Sherebiya, da Shebaniya,
Hodiya, da Bani, da Beninu.
14-27Shugabannin jama'a kuwa, su ne Farosh, da Fahat-mowab,
Elam, da Zattu, da Bani,
Bunni, da Azgad, da Bebai,
Adonaija, da Bigwai, da Adin,
Ater, da Hezekiya, da Azzur,
Hodiya, da Hashum, da Bezai,
Harif, da Anatot, da Nebai,
Magfiyash, da Meshullam, da Hezir,
Meshezabel, da Zadok, da Yadduwa,
Felatiya, da Hanan, da Anaya,
Hosheya, da Hananiya, da Hasshub,
Hallohesh, da Filha, da Shobek,
Rehum, da Hashabna, da Ma'aseya,
Ahaija, da Hanan, da Anan,
Malluki, da Harim, da Ba'ana.
Alkawarin da Aka Yi
28Jama'ar Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da masu tsaron ƙofofi, da mawaƙa, da ma'aikatan Haikali, da dukan waɗanda suka ware kansu daga sauran al'umman waɗansu ƙasashe, domin su bi dokokin Allah, su da matansu, da 'ya'yansu mata da maza, da dai duk waɗanda suke da sani da fahimta, 29suka haɗa kai da 'yan'uwansu, da shugabanninsu, suka rantse, cewa la'ana ta same su idan ba su kiyaye dokokin Allah waɗanda ya ba bawansa Musa ba. Suka rantse za su kiyaye, su aikata umarnai, da ka'idodi, da dokokin Ubangijinmu.
30 # Fit 34.16; M.Sh 7.3 Suka ce, “Ba za mu aurar wa mutanen ƙasar da 'ya'yanmu mata ba. Ba kuma za mu auro wa 'ya'yanmu maza 'ya'yansu mata ba.
31 # Fit 23.10,11; L.Fir 25.1-7; M.Sh 15.1,2 “Idan kuma mutanen ƙasar sun kawo kayayyaki da hatsi don sayarwa a ranar Asabar, ba za mu saya ba, ko kuma a wata tsattsarkar rana.
“A kowace shekara ta bakwai ba za mu girbe amfanin gonakinmu ba, za mu kuma yafe kowane irin bashi.
32 # Fit 30.11-16 “Muka kuma anita kowannenmu zai riƙa ba da sulusin shekel a shekara domin aikin Haikalin Allahnmu.
33“Za mu tanadi gurasar ajiyewa, da hadayar gāri ta kullum, da ta ranakun Asabar, da ta amaryar wata, da ta ƙayyadaddun idodi, da abubuwa masu tsarki, da hadaya don zunubi saboda yi wa jama'ar Isra'ila kafara, da dukan aiki na Haikalin Allahnmu.
34“Muka kuma jefa kuri'a wato firistoci, da Lawiyawa, da jama'a a kan kawo itacen hadaya a Haikalin Allahnmu, bisa ga gidajen kakanninmu, a kan ƙayyadaddun lokatai a shekara, don a ƙona hadayu a bisa bagaden Ubangiji Allahnmu, kamar yadda aka rubuta a dokoki.
35 # Fit 23.19; 34.26; M.Sh 26.2 “Wajibi ne kuma mu kawo nunan fari na gonakinmu, da nunan fari na 'ya'yan itatuwanmu kowace shekara zuwa Haikalin Ubangiji.
36 # Fit 13.2 “Za mu kuma kawo 'ya'yan farinmu maza, da na shanunmu, da na tumaki, da awaki, kamar dai yadda aka rubuta a dokoki, haka za mu kawo su a Haikalin Allahnmu, da gaban firistocin da suke hidima a Haikalin Allahnmu.
37 # L.Ƙid 18.21 “Za mu kuma kawo hatsinmu na fari kullum, da sadakokinmu, da 'ya'yan itatuwanmu, da sabon ruwan inabi, da mai, a gaban firistoci, a shirayin Haikalin Allahnmu.
“Za mu kuma ba Lawiyawa zakar amfanin gonakinmu, gama Lawiyawa ne suke tara zaka a garuruwanmu na karkara. 38#L.Ƙid 18.26 Firist kuwa daga zuriyar Haruna zai kasance tare da Lawiyawa sa'ad da suke karɓar zakar. Lawiyawa kuma za su fid da zaka daga cikin zakar da aka tara musu, su kawo ɗakin ajiya na Haikalin Allah. 39Gama jama'ar Isra'ila da Lawiyawa za su kawo sadakoki na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, a ɗakin ajiya inda tasoshin Haikali suke, da gaban firistocin da suke hidima, da masu tsaron ƙofofi, da mawaƙa.
“Ba za mu ƙyale Haikalin Allahnmu ba.”

Currently Selected:

Neh 10: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in